1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da gwamnati a Bangladesh

August 2, 2024

A kalla mutane 20 ne suka jikkata a arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a Bangladesh, yayin da jama'a ke boren nuna kin jinin gwamnatin Firanminista Hasina.

Dubban al'ummar Bangladesh na neman Firanminista Hasina ta yi murabus
Dubban al'ummar Bangladesh na neman Firanminista Hasina ta yi murabusHoto: DW

Masu boren dai na neman firanminista Bangladesh, Hasina ta sauka daga mukaminta tare da neman 'yanci ga iyalan mutum 150 da aka kashe lokacin zanga-zanga dalibai kan tsarin daukan aiki a kasar. An ruwaito cewa, jami'an 'yansanda sun tarwatsa masu zanga-zangar da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashen roba a arewa maso gabashin garin Habibganj.

Karin bayani: Daliban Bangladesh sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga

Rikicin da kasar ta fada a wannan lokacin shi ne bore mafi girma da gwamnatin Hasina ke fuskanta, bayan wata zanga-zangar da aka yi a lokacin da ta yi tazarce a karo na hudu a kan karagar mulkin kasar, sakamakon lashe zaben watan Janairun 2024 da 'yan adawa suka kauracewa.