Bangui na fiskantar barazanar tsaro
November 22, 2013Ƙasar Faransa ta ce, mai yiwuwa wani kisan kiyashi ya faru a ƙasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Faɗa dai ya ɓarke tsakanin ƙungiyar Seleke da ke da rinjayen musulmai wanda kuma su ka karɓi ikon gwamnatin ƙasar a barar, a ɗaya gefen da kuma 'yan bindiga da ke samun goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Francois Bozize, waɗanda su ka ɗauki makamai don kare kiristoci. Ministan harkokin wajen ƙasar Faransa Laurent Fabius ya faɗa wa gidan talabijin ɗin ƙasar cewa, yanayin da ake ciki a Bangui baya kan tsari. Inda ya bayyana fatan MDD da ƙungiyar Tarayyar Afirka za su amince da shiga tsakani. An dai tura wata tawaggar kiyaye zaman lafiya a Bangui, amma bata da wani ƙarfi. A yanzu haka dai an yi kone-ƙonen Masallatai da Coci-Coci. Kiristoci dai su ne kashi 50 cikin ɗari na al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Zainab Mohammed Abubakar