1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bankado badakala a harkar mai a Nijar

Gazali Abdou Tasawa
August 19, 2019

A Jamhuriyar Nijar 'yan kasar na ci gaba da mayar da martani kan badakalar cin hanci ta sama da biliyan 14 da rabi na kudin Cefa da Hukumar HALCIA ta bankado musamman a matatar man fetir ta SORAZ

Wata matatar mai a Ghana
Mun yi amfani da tsohon hoto na wata matatar mai a GhanaHoto: imago/Xinhua


A Jamhuriyar Nijar 'yan kasar na ci gaba da mayar da martani kan badakalar cin hanci da rashawa ta sama da biliyan 14 da rabi na kudin Cefa da hukumar yaki da cin hanci ta kasar ta HALCIA ta bankado musamman a fannin kasuwancin man fetir da kasar ke hakowa da kuma a fannin aikin kustom. Hukumar ta HALCIA ta bayyana wannan labari ne a loakcin wani taron manema labarai da ta gudanar a makon da ya gabata a karkashin jagorancin Shugabanta Abdourahamane Gousmane.

Hukumar ta HALCIA ta ce a wannan shekara ta 2019 kadai an shigar da kararraki 180 na cin hanci da rashawa a gabanta. Kuma binciken da ta gudanar ya ba ta damar bankado badakalar kudi ta sama da miliyan dubu 14 da 500 na Cefa kwatankwacin miliyan 22 na Euro da kasa ta yi asararsu a sakamakon karkatar da akalarsu da wasu suka yi. Daga cikin wadannan kudade, sama da miliyan dubu uku sun salwanta a fannin kudaden haraji da kamfanoni da sauran 'yan kasuwa na kasar ke kin biya. Amma babbar badakala ta kudi sama da miliyan dubu 11 na Cefa ta wakana ne a fannin aikin hakar man fetir da Allah ya huwace wa kasar.  

Foumakoye Gado ministan mai na Jamhuriyar NijarHoto: DW/A. M. Amadou

Matsalar ta samo tushe ne daga babbar matatar mai ta kasar ta SORAZ da ke a yankin Damagaram inda hukumar ta HALCIA ta ce ta gano wata cuwa-cuwa da ke gudana a fannin jigilar man daga Nijar zuwa Mali da Bukina Faso da kuma Najeriya inda wasu ke karkatar da akalar wasu tankokin man da aka aika zuwa wadannan kasashe. Rahoton Hukumar ta HALCIA ya nunar da cewa kaso takwas daga cikin dari na tankokin man da ake aikawa zuwa Mali da Burkina Faso da kuma kaso 10 daga cikin dari na wadanda ake aikawa Najeriya ba sa isa masaukinsu. Hukumar ta HALCIA ta ce a yanzu dai ta yi nasarar karbo miliyan 500 na Cefa daga cikin hakkokin gwamnatin da ke a hannun jama'a.

Tuni dai wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a da na yaki da cin hanci na kasar ta Nijar suka soma kiraye-kirayen ganin gwamnati ta dauki matakin shigar da takardun dabakalar da Hukumar ta HALCIA ta bankado a gaban kuliya domin a gurfanar da wadanda ke da hannu a cikin da kuma hukunta su gwargwadon laifinsu. Yanzu dai za a iya cewa HALCIA ta yi nata aiki, dan haka wukka da nama na a hannunn gwamnatin Nijar na daukar mataki gurfanar da mutanen a gaban kotu idan dai har da gaske take cewa tana yaki da cin hanci da rashawa a kasar. 

Mun yi amfani da tsohon hoto na wata matatar mai a ChadiHoto: Desirey Minkoh/AFP/Getty Images
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani