Bankin AfDB zai ba wa Côte d'Ivoire Euro miliyan 770
December 16, 2016![Zentrale der Afrikanischen Entwicklungsbank](https://static.dw.com/image/18486848_800.webp)
Talla
Hukumar zartarwa ta Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ta amince da bada bashi na Euro miliyan 770 ga kasar Côte d'Ivoire, kudaden da za a yi amfani da su wajen gyara hanyoyin mota a birnin Abidjan cibiyar hada-hadar kasuwancin kasar da ma samar da gadoji kamar yadda bankin ya bayyana a ranar Juma'ar nan.
A cewar Amadou Oumarou daraktan da ke lura da harkokin da suka shafi sufuri a bankin, wannan zai taimaka wajen kawo raguwar yawaitar cinkoson ababan hawa a titunan birnin, a rage aukuwar hadura kana a samu iska tsaftatacciya a yankin.