Sabon bankin raya kasashe masu tasowa
July 21, 2015Talla
Sabon bankin raya ƙasashe na ƙasashen Ƙungiyar BRICS wanda tattalin arzikinsu ke haɓaka da sauri ya buɗe koffofinsa a birnin Shangai na ƙasar China.Bankin wanda ake yi wa laƙabi da sunan New Developement Bank zai kalubancin manyan hukumomin kuɗi na ƙasashen yammacin dniya na asusun ba da lamuni IMF da kuma Bankin duniya.
Ƙasashen na BRIC waɗanda ke zama kishi 40 cikin dari na yawan al'ummar duniya waanda suka haɗa da Brazil da Chinina da Indiya da Rasha da kuma Afirka ta Kudu .Sun yanke shawarar girka bankin a shekarun 2013 wanda ke da jarin dala bliyan 100 kuma China ita ce mai yawan hannun jarin da kishi 30 cikin dari