1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

CBN ya bayyana Najeriya da rudanin tattalin arziki

Ubale Musa/YBMay 25, 2016

A cewar bankin tun a cikin kusan shekaru 25 din da suka gabata dai kasar ta Najeriya ba ta kalli matsi da ma hali irin na tattalin arzikin da ta kai na shekarar da muke ciki a halin yanzu ba.

Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos
Naira kudin da Najeriya ke amfani da ita na ci gaba da samun koma baya a kasuwa.Hoto: Getty Images

A wani abun da ke zaman alamu na kara lalacewar lamura ga batu na tattalin arzikin tarrayar Najeriya, babban bankin kasar na CBN ya ce tattalin arzikin kasar na fuskantar barazana ta durkushewa a karon farko.

Tun a cikin kusan shekaru 25 din da suka gabata dai kasar ta Najeriya ba ta kalli matsi da ma hali irin na tattalin arzikin da ta kai na shekarar da muke ciki a halin yanzu ba. A karon farko dai kasar na fuskantar asarar da ta kai kusan kaso hudu a cikin dari na tattalin arzikin kasar a farko na watanni uku na shekarar da muke ciki.

To sai dai kuma dorewar yanayin sakamakon gaza kaiwa ga samun kasafin kudi bisa na lokaci, sannan kuma da share daukacin shekarar da ta shude ana wadaka da sunan zabe na siyasa, game kuma da matakan tsaurara samun kudin shigar kasashen waje domin amfani na kamfanoni dai na neman jefa tattalin arzikin kasar cikin barazana a fadar babban bankin kasar na CBN.

Shugaba Buhari da Christine Lagarde ta IMF da Godwin Emefiele shugaban babban bankin Najeriya a AbujaHoto: Reuters/A. Sotunde

Duk da cewar dai sabbabin mahukuntan na Abuja sun dauki lokaci suna karatun raba kafa, dogaro da harkar man fetur sannan kuma da fasa bututun man fetur a yankin Niger Delta ya sanya kasar ta yi nisa a cikin matsatsin da ke zaman irinsa mafi zafi a shekara da shekaru.

Abun kuma da ya kai tattalin arzikin kasar zuwa kasa da kaso guda cikin dari a karon farko. Malam Yusha'u Aliyu dai na zaman masani na tattalin arzikin kasar kuma sabon yanayin kasar a fadarsa na da ruwa da tsaki da yadda gwamnatin ke tsoma baki a cikin harkoki na kasuwa cikin kasar a halin yanzu.

Ginin babban bankin Najeriya

Rufe kofofi na shigowa da abinci cikin a tsakar rani dai ya yi tasirin wajen hauhawar da ta jima babu irinta, ga batun na farashi kama daga abincin ya zuwa bukatu na yau da na gobe.

Ko bayan nan dai halin berar da a ke zargin magabata na gwamnatin da tafkawa ya tilasta Abujar gabatar da jeri na matakai da nufin ceton Naira da kuma gina hada hadar cikin gida.

To sai dai kuma a cewar kakaki na gwamnatin Malam Garba Shehu dogaro ga hajjar mai kaco kam na zaman ummul aba'isin sabon yanayin da a cewarsa ya kai kasar zuwa inda ake.