1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

BANKIN DUNIYA DA SHIRIN YAKAN TALAUCI A DORON KASA

YAHAYA AHMEDApril 26, 2004

A taron bankin duniya da aka kammala jiya a birnin Washington, wakilai sun nuna damuwarsu ga irin tafiyar hawainiyar da ake yi wajen aiwatad da shirin nan na yakan talauci a duniya. Duk bangarorin da wannan batun ya shafa, wato kasashe masu ba da taimako da kasashe masu karbar taimakon, na da tasu rawar takawa, wajen cim ma gurin da gamayyar kasa da kasa ta sanya a gaba a cikin shekara ta 2000, na rage yawan matalauta zuwa rabin adadin da ake da shi yanzu a duniya, kafin shekara ta 2015.

Heidemarie Wieczorek-Zeul, ministan ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta Jamus, a taron bankin duniya a birnin Washington
Heidemarie Wieczorek-Zeul, ministan ma'ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta Jamus, a taron bankin duniya a birnin WashingtonHoto: AP

Daya daga cikin manyan gurin da gamayyar kasa da kasa ta sanya a gaba, wanda kuma take son ta cim ma kafin shekara ta 2015 shi ne: ko wane yaro a doron kasa ya sami damar halartar makaranta, ko da ta firamare ce. Amma, bisa tafiyar hawainiyar hawainiyar da ake yi yanzu, za a iya ganin cewa kasashe matalauta da dama na nesa daga cim ma wannan gurin. Game da wannan halin da ake ciki, da kuma daukan matakan ba da kaimi wajen aiwatad da shirye-shiryen da aka tsara ne, wasu kasashe masu arzikin masana’antu, a cikinsu kuwa har da Jamus, suka dau alkawari, a taron bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya da aka kammala jiya a birnin Washington, na ba da karin taimakon kudade, don ci gaba da manufar yakan talauci a duniya.

Ministan ma’ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta nan Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul, ta ce gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar kara gudummuwar da take bayarwa a ko wace shekara, don ganin cewa an sami ci gaba a yunkurin da ake na aiwatad da shirye-shiryen da aka tsara. Kamar dai yadda ta bayyanar:-

"Daukar matakan ganin cewa, duk yara a doron kasa sun sami damar shiga makarantu kafin shekara ta 2015, wata muhimmiyar manufa ce, wadda kuma za a iya daukarta kamar zuba jari ne a yunkurin inganta makoman yaran, da kuma makoman kasashe masu tasowa. Muna goyon bayan wannan shirin, kuma, mun ba da alkawarin cewa, za mu kara yawan tallafin kudin da muke bayarwa a ko wace shekara, da Euro miliyan dari da 20, daga nan har zuwa shekara ta 2007."

Idan dai aka yi la’akari da kudaden da ake bukata don cim ma gurin, kamar yadda aka shirya, to wannan gudummuwar da Jamus ta ce za ta bayar, ba wani abin a zo a gani ba ne. Wasu kasashe kamarsu Holland, sun fi nuna fahimtar matsalolin da ake huskanta, sun kuma dau alkaearin ba da taimako mai tsoka. Ita kasar Holland dai, bisa cewar ministanta mai kula da ba da taimakon raya kasashe, ta ce za ta ba da karin taimakon kudi na Euro miliyan dari 6 a ko wace shekara, har tsawon shekaru uku nan gaba, tamkar gudummuwarta ga yunkurin cim ma wannan gurin.

Wani kiyasin da kungiyar sa kan nan OXFAM ta yi, na nuna cewa, har ila yau dai ana da gibin dola biliyan 5, wanda kuma ya kamata a cike, kafin a iya cim ma gurin bai wa duk yara a duniya damar halartar makaranta, kafin shekara ta 2015. Ban da wannan kuma, akwai sauran shirye-shirye, kamarsu samar wa duk yankuna na duniya ruwan sha mai tsabta, da kuma rage yawan talauci zuwa rabin adadinsa na yanzu, kafin wa’adin shekara ta 2015 ya cika.

A ganin shugaban bankin duniya James Wolfinsohn, kudin da za a kashe wajen yakan talauci kawai, zai kai dolar Amirka biliyan 50. Ya kara da cewa:-

"Kamata ya yi kasashe masu tasowa ma su ba ta su gudummuwa wajen cim ma wannan gurin. Abin da za su iya yi a nan shi ne, yi wa kafofin shari’a da cibiyoyin harkokin kudinsu garambawul, sa’annan kuma su tashi haikan wajen yakan cin hanci da rsahawa. Kasashe mawadata kuma, wajibi ne garesu, su goyi bayan yunkurin da kasashe masu tasowan ke yi, su kuma bude kasuiwanninsu ga kayayyaki daga wadannan kasashen, sa’annan su kara taimakon da suke bayarwa, ga shirye-shiryen raya kasa. Yafe wa wasu kasashen basussukansu na da muhimmanci kwarai a wannan huskar."

James Wolfinsohn, ya kara bayyana cewa, an cim ma wani daidaito tsakanin bankin duniyar da asusun ba da lamuni na duniya, inda za a dinga bai wa kasashe masu tasowa tallafi, wajen aiwatad da shirye-shiryensu, maimakon basussuka. Amirka ma ta ce a shirye take, ta goyi bayan wannan tsarin.

Ministar ma’ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya kasashe ta Jamus, Heidemarie Wieczorek-Zeul, ta nanata cewa, shirin nan na yafe wa kasashe mafi talauci a duniya basussukansu, wanda aka yarje a kansa a taron rukunin G-8 da aka yi a birnin Kolon a shekarar 1999, ya fara haifad da kyakyawan sakamako:-

"Mun dai lura da cewa, shekara biyar bayan amincewa da shirin yafe wa wasu kasashe basussukansu, an fara samun nasar. A kalla dai, kasashe 27 da suka shirin na kan hanyar samun ragowar basussukansu da kashi 2 bisa 3. Abin farin ciki ne ganinn cewa, kasashe 13 kuma, sun cim ma gurin sauke nauyin duk basussukansu, a karkashin wannan shirin."

Har ila yau dai, akwai wasu kasashen kuma, kamarsu Laberiya, inji ministan, wadanda saboda rikice-rikcen cikin gida, ba su sami damar cika ka’idojin samun ragowar basussukansu ba. Kamata ya yi kuwa, a kara musu lokaci.