Afirka ta samu tallafin kudin yaki da yunwa
June 22, 2022Talla
Shirin bankin duniyar ya zai mayar da hankali ne kan kimanin mutane fiye da miliyan 66 a wadannan yankunan Afirka da aka yi ahsashen za su fuskanci matsalar abinci a watan Yuli na shekarar 2022.
Za kuma afara aiwatar da shirin ne daga kasar Habasha, inda kusan mutane miliyan 22 da 700 ke fama da karancin abinci sanadiyyar matsalar fari, sai kuma kasar Madagaska inda mutane miliyan 7 da 800 suma ke cikin bukatar agajin abinci na gaggawa sakamakon rashin ruwa da ya haifar da fari a kudancin kasar.