1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Bankin Libya ya yi barazanar dakatar da aikinsa

August 18, 2024

Babban bankin kasar Libya ya ce zai dakatar da aiki tare da rufe dukkan rassan bankunan a fadin kasar har sai an saki guda daga cikin manyan jami'an bankin da aka yi garkuwa da shi a Tripoli.

Firaiministan Libya Abdul Hamid Dbeibah, da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen yamma
Firaiministan Libya Abdul Hamid Dbeibah, da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen yammaHoto: Yousef Murad/AP Photo/picture alliance

Babban bankin wanda shi ne kadai kasashen duniya suka amince da shi wajen alkinta kudaden albarkatun man fetur da tattalin arzikin kasar da ke da gwamnatoci guda biyu da basa ga maciji da juna a Tripoli da Benghazi ya dogara da shi. Sanarwar da bankin ya fitar ya ce wasu batagari ne suka sace babban jami'in bankin Musaab Muslam, da ke shugabantar sashen sadarwa na bankin.

Karin bayani: Rikicin Libya har yanzu ba ta sauya zani ba

Jakadan Amurka a Libya Richard Norland, ya ce basa goyon bayan duk wani yunkuri na canza ma'aikatan bankin, kuma yin hakan ka iya dakatar da tallafi da kuma samun damar zuba hannun jari ga kasar ta Libya. Jakadan na martani ne kan bayanan da ke cewa wasu gungun mutane na kai komo a harabar babban bankin da ke Tripoli.

Karin bayani: Libiya: Hako fetur na fuskantar koma baya

Kasar Libya ta dare gida biyu da bangaren da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin Abdulhamid al-Dbeibah, a birnin Tripoli.  Kazalika shiyyar gabashin kasar na karkashin shugabancin Janar Khalifa Haftar da ke sansani a birnin Benghazi.