1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin tarayyar Turai zai fanshi bashjin wasu ƙasashen euro.

August 8, 2011

Babban Bankin ƙasashen Turai ya ce ya na shirin fansar bashin da ake bin wasu ƙasashen da ke amfani da takardar kuɗin euro domin daidaita al'amura a kasuwanin hada-hadar hannayen jari na duniya

Cibiyar Bankin tarayyar turai a FrankfurtHoto: picture alliance/dpa

Cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a jiya lahadi da maraice, ya ce wannan wata hanya ce ta shawon kan matsalar bashi da ta addabi wasu ƙasshen turai, wanda kuma ke naman haifarwa Euro Illa. Sanarwar ta zo ne bayan da ƙasashen Spain da kuma Italiya suka bayyana cewar za su gaggauta matakan tsuke bakin aljuhu da suka sa a gaba, domin shawon kan matsalar koma bayan tattalin arziki da suke barazanar faɗawa ciki. Babban Bankin na Turai ya yaba wannan mataki da suka ɗauka, tare da nunar da mahimmacin cika biyan bashin da ke kansu ba wai da sunan magance matsalar koma bayan arziki ba, amma domin cika alƙwarin da suka yi tun da farko. A ɗaya hanun kuma ruƙunin ƙasashe nan bakwai da suka fi ƙarfin tattalin arziki sun fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa, inda suka bayyana cewar za su bayar da gudunmawa domin a samu daidaito a al'amuran tattalin arziki a duniya baki ɗaya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita : Abdullahi Tanko Bala