1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barack Obama ya amince ya zama ɗan takarar Democrat

September 7, 2012

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi a ƙarshen taron jam'iyyar da a ka yi a North Carolina

U.S. President Barack Obama waves as he arrives to address delegates during the final session of the Democratic National Convention in Charlotte, North Carolina, September 6, 2012. REUTERS/Jason Reed (UNITED STATES - Tags: POLITICS ELECTIONS) // Eingestellt von wa
Hoto: reuters

A jawabin da shugaba Obama ya yi a gaban wakilan jam'iyyar ta Democrat da kuma wasu dubun bubatar jama'ar a Charlotte ya buƙaci jama'ar da su zaɓi jam'iyyar ta Demokrat a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe a wa'adi na biyu.Obama wanda ya yi gargaɗin cewar Amirka za ta iya tsallake wahalolin da ke a gabanta tare da cimma kyaukyawar makomma ta tattalin arziki a gaba ga irin ƙalubalan da ƙasar ta ke fuskanta wanda tun a sheka ta 2008 ya faro da iƙirarin neman canji.Ko da shi ke ya yi alƙawarin kawo sauye sauye ta fuskar tattalin arzikin tare da ƙirƙiro sabbin guraban ayyukan yi, amma shugaban ya ce ba za a iya cimma biyan buƙata ba nan ta ke, dolle sai an jira ɗan lokacin kafin magance matsalolin da suka taru a tsawon shekaru gomai ga ƙasar.

Obama ya ce zaɓen zai kasance zaɓi ga al'umma a kan burin tattalin arziki

Zaɓen da zai gudana wani ma'auni ne da ke da banbbanci a ɓangarorin biyu daban ,ya ce wani zaɓi ne ga masu fafutukar nemman kyautata rayuwar al'umma mara sa ƙarfi da masu ɗan ƙarfi. Da kuma waɗanda ke neman ƙara zu´ba ruwa a cikin kogi ainafin masu haƙidar ƙara azurta masu arziki a waje da ciki ta fuskar ƙarfin tattalin arzikin da duniya ba ta yardda da shi ba, sannan ya ƙara da cewar.''zaɓi na gare ku ;ko dai ku yardda a ɗauki ayyuka a kai waje mu yi asarar kuɗaɗen haraji ko kuma a samar da ayyukan yi a nan Amirka.Wannan karin magana dai ya na zama shagube ga jam'iyyar 'yan Republicain wanda a cikin jawabin Obama ya yi suka a gare su. Allah kuli hali dai shekaru na gaba masu zuwa; zasu kasance mafi tarihi da kuma buri na ƙaddamar da muhimman tsari na tattalin arziki da jam'iyyar ta Demokrat ta zayana.

Barack Obama da iyalen saHoto: Reuters

Manufofin tattalin arziki na Obama

Wanda a ƙarƙashin manufofin shugaban ya yi alƙawarin kawo sauye sauye ta fuskar tsaro ,da dai saraun batutuwa masu mahmmanci na tattalin arzikin ƙasar wanda ya yi kira ga jama'a da su ba da haɗin kai domin cimma manufofin.Ya ce ''ku haɗa ƙarfin da ƙarfe a wuri guda domin mu cimma waɗannan manufofi ga ƙasar mu na samar da makamshi da illimi da rage giɓi da ake samu da kuma kyautata al'ammuran tsaro''..A fili ta ke dai Obama na da tsarin da ya ke son ya ƙaddamar kafin nan da shekara ta 2014 inda har ya sami nasara a zaɓen ;waɗanda su ne samar da ayyuka ga matasa har miliyion ɗaya tare da ninka yawan irin hajojin da Amirka ta ke fid 'da wa a waje ta hanyar kasuwanci da rage yawan abin da ƙasar take shigowa da shi.

Barack Obama da Bill ClintonHoto: Reuters

Amurkawa na jiran samun sauyi daga Shugaban

Wannan wata ɗaliba ce da ke karatu a Texas kuma ta yi yardda tare da yin imanin da alƙawarin da Obama ya yi na kyautata rayuwar al'umma a cikin shekaru masu zuwa.Ta ce ''ɗan takarar ɗallibai ne da matasa saboda ya san cewar ilimi na da mahimmanci da kuma kare hakin mata da kyautata sha'anin kiwon lafiya''.A yanzu dai za a iya cewar kishiri ya kama kan kaza zam zam , sai dai kuma sannin gabi sai Allah, amma dai kawo yanzu masu hasashe a kan al'ammuran zaɓen na cewar ɗan takarar na jam'iyyar Demokrat da na Republicain suna tafe kafaɗa da kafaɗa, wajan hasashen samin nasara a zaɓen.

magoya bayan jam'iyyar DemokratHoto: Reuters

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe

Daga ƙasa za a ya sauraron wannan rahoto