Barack Obama ya soma kampe
September 4, 2012![President Barack Obama and former President Bill Clinton stand together on stage at the end of a campaign event at the New Amsterdam Theatre, Monday, June 4, 2012, in New York. (Foto:Carolyn Kaster/AP/dapd)](https://static.dw.com/image/16029799_800.webp)
Na gaba ƙadan ne yan jam'iyyar demokrat a Amirka zasu gudanar da wani gamgamin siyasa a Charlotte da ke cikin jihar Nord Carolina.A mataki na farko na farfagandi domin ƙaddamar da takarar Barack Obama a zaɓen shugaban ƙasar na watan Nuwanba da ke tafe,gangamin wanda za a kwashe kwanaki ukku ana yin sa, an shirya mai ɗakin shugaban ƙasar Michelle Obama.
Za ta yi jawabi na farko ga al'ummar yankin, domin samun goyon bayan su, kafin a ranar alhamis Obama ya yi jawabin ƙarshe a cikin filin ƙwalon kaffa , na garin inda ake sa ran sama da mutane dubu 65 zasu halara.Masu yin sharhi akan al'amura dai na cewar yan takarar biyu a zaɓen shugaban kasar wato Barack Obama da Mit Romney na tafe kafaɗa da kafaɗa ta fuskar jin ra'ayoyin jama'a dangane da wanda zai sami nasara.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar