1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Barakar gwamnatin kawancen Jamus ta janyo cire ministan kudi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 7, 2024

Rikicin siyasa na zuwa ne a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke tafiyar hawauniya duk da cewa shi ne mafi karfi a nahiyar Turai.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz tare ministan kudi da ya tsige Christian Lindner
Hoto: CHRISTOF STACHE/AFP

Bayan shafe makonni ana tattaunawa kan makomar tattalin arzikin Jamus, shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz ya sauke ministan kudi Christian Lindner na jam'iyyar FDP mai sassaucin ra'ayi daga mukaminsa. Da yake jawabi kan dalilin daukar wannan mataki, Scholz ya ce Lindner na yawan saba alkawarun da ya dauka lokacin da suka hada gwiwa wajen kafa gwamnati, saboda haka aikin ba zai yiwu ba a irin wannan yanayi.

Shi dai Christian Lindner, ya bukaci a yi sauye-sauye a fannin tattalin arziki, amma sauran jam'iyyu biyu na kawancen gwamnatin Jamus na adawa da wannan mataki.

Karin bayani:Kawancen jam'iyyun CDU/CSU na kan gaba a zaben EU da aka kammala

Wannan rikicin siyasa na zuwa ne a daidai lokacin da tattalin arzikin Jamus ke tafiyar hawauniya, duk da kasancewarsa mafi karfi a nahiyar Turai. Shugaban gwamnatin Jamus Scholz ya bayyana cewar majalisar dokoki ta Bundestag za ta kada kuri'ar amincewa da gwamnatinsa ko akasin haka a ranar 15 ga Janairun sabuwar shekarar 2025 mai kamawa.

Wannan dambarwar za ta iya share fagen gudanar da zaben gaba da wa'adi na 'yan majalisar dokokin Jamus da aka shirya gudanarwa a kakar shekarar 2025 zuwa watan Maris din shekarar 2025.