1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazana ga al'amuran yawan buɗe ido a Masar

July 4, 2012

Zuwan sabon shugaban ƙasar Mohammed Mursi akan karagar mulki zai iya janyo koma baya ga sha'anin shaƙatawa, saboda haƙidarsa ta musulumci

An Egyptian soldier guarding the border between Egypt and Israel near the Hilton Taba hotel in Egypt on Friday, 08 October 2004 after the bomb attack in the Egyptian tourist resort of Taba the evening before. Foto: PAVEL WOLBERG dpa
Hoto: picture-alliance/dpa

Bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ƙasar Masar wanda dan takara jam'iyar yan uwa musulumi Mohammed Mursi ya sami nasara yanzu haka baƙi yan ƙasashen waje na da fargaba zuwa yawan shaƙatawa a ƙasar saboda sauyi da aka samu na gamnatin da ke kishin addinin da ma wasu yan ƙasar wadanda suke ci abinci ta wannan fannin

Kashi ɗaya bisa shidda na kuɗaɗen shigar da ake samu a ƙasar ta Masar na shigowa ne ta hanyar lamarin yawan buɗe ido wanda ke ɗaya daga cikin shika shika na tattalin arziki da ke zaman mataki na ukku.Fargaban da jama'a galibi baƙi yan ƙasahen yammancin duniya da ke ziyarta ƙasar suke da shi ne na sauyin al'adu ta hanyar saka tufafi da ma haramci na shan barasa da akan iya samu.

Wannan kuma na ƙara saka shakku ga sauran jama'ar ƙasar ta Masar da ke cin abinci ta wannan hana,Ekrami Latif ɗan shekaru kimani 36 da haifuwa wani ma'aikacin wani wurin shaƙatawar ne da ke bakin teku na garin Gouma wanda ke yi wa masu yawan buɗe idon jagora a cikin zirganiyar su ta yau da gobe ''ya ce haƙiƙa muna jin tsoron zuwan Mursi ya;sa a masu yawan shaƙatar na ƙashen duniya su canza sheƙa su koma zuwa cikin wasu ƙasahe inda zasu samu karɓuwa fiye da nan Masar.

Fargaban al'ummar Masar akan zuwan Mursi kan karagar mulki

a garin na gouma wanda musulumi da krista suke zune girma da arziki shekara da sekru yawanci jamaar sun kada kuria ne ga abokin hammayar mohammed mursi wata ahmed chafik saboda ko wannan larurura da suke gananin na iya zama babbar barazana ga tattalin arzikin ƙasar.Kuma tun can da farko kafin a rusa sabuwar majalisar dokokin har yan jam'iyar ta yan uwa musulumi sun fara ambato batun sayar da giya a ƙasar. wata yar ƙasar Hollande Annemarie Bakker wacce ta taɓa zuwa har so fuɗu a ƙasar ta Masar ta yi ƙorafin cewar za su iya daina zuwa ƙasar inda an canza abubuwa.''ta ce idan ba za a bar mu mu sha giya ba ;mu je Pikinik ta ce ba zamu sake komawa Masar ɗin ba, ta ce amma a gaskiya ƙasa ce da na ke sha'awa ƙwarai.

Mohamed MursiHoto: Reuters

Jama'a na jiran samu sauyi ta fannin al'umuran shaƙatawa tare da Mursi

A cikin jawabi da ya yi sa lokacin da aka ƙaddamar da bikin rantsar a shi shugaban na Masar Mohammed Mursi ya sha alwashin haɓaka al'amuran shakatawa harma su fi na lokacin da , to sai dai jama'a na jiran su gani a ƙasa,Adam Mahmoud shugaban wurin shaƙatawar na Gouma ya ce suna sa ran cikka alƙawari ga Mursi.''ya ce idan kana nema wata ƙasa wacce talauci da zaman kashe wondo ya yi wa kanta to sai Masar ya ce tilas ne hugaban yayi wani hoɓasa domin samun ci gaba.

Hoto: AP

A shekara ta 2011 ofishin minstan yawan buɗe ido na ƙasar ta Masar ya ce ya samu ƙaruwa kuɗaden shiga daga ɓangaren yawan buɗe idon da kashi 30 cikin ɗari fiye da shekarar bara.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu