1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazana ga Rasha kan rikicin Ukraine

March 13, 2014

A dai dai lokacin da wa'adin kada kuri'ar raba gardama da majalisar dokokin yankin Kirimiya na kasar Ukraine ta sanya ke kara karatowa, shugabar gwamnatin Jamus ta yi gargadi ga Rasha.

Hoto: Reuters

Majalisar dokokin yankin na Kirimiya dai ta sanya ranar Lahadi 16 ga wannan wata na Maris da muke ciki a matsayin ranar da za'a kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a a yankin kan ballewa daga Ukraine din da kuma komawa karkashin ikon kasar Rasha, sai dai kuma lamarin na ci gaba da samun martani daga kasashen ketare inda Jamus ta gargadi Rashan da cewa za ta fuskanci gagarumar barazana ta fannin siyasa da tattalin arziki in har bata canza matakan da take dauka kan rikicin Ukraine din ba. Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ce ta bayyana hakan a yayin da take jawabi a gaban majalisar dokokin kasar ta Bundestag inda ta ce baki dayan kasashen nahiyar turai a shirye suke su duba yiwuwar kakabawa Rashan takunkumin karya tattalin arziki in har bukatar hakan ta taso.

Zafafan kalamai a karon farko

Wannan dai shine karo na farko da Merkel ta yi amfani da kalamai masu tsauri a kan mahukuntan na Moscow tun bayan da aka fara takaddama kan makomar yankin na Kirimiya dake kasar Ukraine din, kuma jawabin nata ya cire duk wani shakku da ake da shi kan cewa Jamus za ta iya kaucewa daukar tsauraran matakai a kan Rashan. Merkel ta kara da cewa matakan da Shugaba Vladimir Putin na Rashan ke dauka zai iya janyo gagarumar matsala ga kasar Ukraine da ma sauran kasashen dake nahiyar Turai tana mai cewa....

Masu zanga-zanga a Kirimiya dake goyon bayan RashaHoto: Getty Images

"Ba wai muna ganin matakan da Rashan ke dauka bane a matsayin barazana kasancewar mu makwabta ga Rashan, ba kuma zai canza dangantakar dake tsakanin Rashan da kungiyar Tarayyar Turai bane kawai, a'a zaima shafi Rasha matuka ta fuskacin tattalin arziki da kuma siyasa"

Shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ta ce kokarin da tayi na sanya Shugaba Putin na Rasha ya tattauna da gwamnatin rikon kwarya ta kasar Ukraine, da Moscow ke zargi da kifar da halastacciyar gwamnati ta Shugaba Viktor Yanukovych ya ci tura kuma lokaci na kurewa ta kuma kara da cewa.....

"Maganar gaskiya ita ce babu wani a cikinmu da yake fatan ganin mun dauki matakan kakabawa Rasha takunkumi, amma a shirye muke kuma mun dauki aniyar yin hakan in har babu wata hanya da zamu iya kaucewa"

Danganta Kirimiya da Kosovo

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta ce babu yadda za'a yi a danganta kasar Ukraine da kuma Kosovo da ta balle daga tsohuwar kasar Yugoslavia a shekara ta 2008, inda ta ce dolene a tabbatar da kasancewar Ukraine a matsayin kasa mai cikakken iko. Shin ko za'a iya danganta kuri'ar raba gardamar da ake shirin kadawa a yankin na Kirimiya da wacce aka kada a Kosovo a lokacin da ta balle daga kasar Sabiya ko kuma wadda Bosniya Hezgobina da kuma sauran kasashe suka kada? A wata hira da ya yi da tashar DW Farfesa Franz-Lothar Altmann na jami'ar Bukarest babban birnin kasar Romaniya wanda kuma ke zaman mammba a hukumar daraktoci ta gidauniyar Bertelsmann dake nan Jamus ya ce......

Masu zanga-zanga a Kirimiya dake adawa da RashaHoto: Genya Savilov/AFP/Getty Images

"Duk kanwar ja ce, sai dai kuma a wannan yanayin in har kana tunani a kan kasar Rasha ne Rasha na da matsala da yankin Ceceniya dake kokarin ballewa daga kasar, sannan a hannu guda kuma tana son ta janye yankin Kirimiya zuwa cikin kasarta, danganta wannan yanayi dana Kosovo a ganina abu ne ba mai yiwuwa ba, babu wani yakini da kasashen duniya ke da shi a kan wannan lamari, yanayin dai na da sarkakiya"

A hannu guda kuma wata jarida ta kasar Rasha ta ruwaito Shugaba Vladimir Putin na cewa zai tattauna da Ukraine domin duba yiwuwar kulla dangantaka a tsakaninsu, inda ya ce ya kamata suyi tunani a kan yadda za su kulla alaka da abokansu dake Ukraine da kuma sauran abokansu dake nahiyar Turai da Amirka. Putin dai ya yi wannan jawabi ne a yayin da yake bude taron majalisar tsaron kasar ta Rasha. Kasashen yamma dai na kokarin dakatar da safarar iskar gas ta bututun da ya ratsa ta kasar Rasha zuwa nahiyar Turai a wani mataki na gurgunta tattalin arzikin Rashan. Sai dai acewar masana matakin ba wai Rashan kadai zai shafa ba harma da sauran kasashen nahiyar Turan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba