1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazana ga tattalin arziƙin Sudan

January 6, 2011

A ranar 9 ga watan Janairu kudancin Sudan za ta tsai da shawarar ko ta ɓalle daga arewaci ko kuma a yi tafiya tare . Ko wane irin tasiri hakan zai yi ga tattalin arziƙin ɓangarorin biyu?

Shirye-shiryen zaɓe a kudancin SudanHoto: picture alliance/dpa

A ranar 9 ga wannan wata na Janairu ne alumar kudancin sudan za su kaɗa ƙuri'ar domin kafa ƙasa mai yacin cin gashin kanta-abin da zai yi tasirin gaske ga zaman lafiya da kuma makomar tattalin arziƙin kasar - arewaci da kudanci ga baki ɗayansu, saboda cewa ɓangarorin biyu suna dogaro ne da juna a fannin tattalin arziƙi.To ko wane irin tasiri raba ƙasar gida biyu zai yi akan tattalin arziƙinsu?

Raguwar kuɗin man fetur

Salva Kiir, shugaban gwamnatin kudancin SudanHoto: AP

Arewacin Sudan dai na fargabar cewa ɓallewar kudanci sai janyo mata asasar kudaden da take samu, saboda cewa daga nan take samun kashi 70 daga cikin ɗari na man fetur. Daga kudaden da ake samu daga wannan hajar ne kuma ake ware kashi 90 daga ciki ɗari na kasafin kuɗin ƙasar . Yarjejeniyar zama lafiya da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu bayan kawo ƙarshen yaƙin basasan kasar, ta tanadi raba kuɗin da ake samu daidai wa daida tsakaninsu. Abda Yahia Abdul Rahman Al Mahdi shugabar kanfanin UNICONS da ke da mazauninsa a birnin Khartoum, kuma tsohuwar ministar kuɗin ƙasar ta yi imanin cewa ɓangarorin biyu za su ci gaba da tafiya tare domin cimma ma wasu bukatun nasu.

Ta ce: "Zan yi matukar mamaki idan har aka kasa cimma wata yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu. Saboda cewa a lokacin da arewaci ke bukatar man fetur, kudanci kuma na buƙatar ababan more rayuwa. Dalili kenan da ya sa na yi imanin cewa babu makawa za a cimma yarjejeniya bayan ɓallewar kudanci. To amma rashin cimma hakan kuma wani abu ne da ka iya janyo ɓarkewar yaƙi."

Shugaba Al-Bashir mai goyon bayan haɗin kaiHoto: AP

Aikin gina bututun man fetur da zai gilma ƙasar Kenya dai aiki ne mai tsadar gaske ga kudanci, da za a shafe aƙalla shekaru uku ana gudanar da shi.

Haɗari ga zaman lafiya

Duk da kuwa tabbacin da Shugaba Al-Bashir ya bayar ana bayyana shakkun cewa ba za a iya aiwatar da raba ƙasar gida a cikin limana ba. A dai shekarar 2005 ne aka kawo ƙarshen yaƙin basasan shekaru 20, da aka kiyacse cewa mutane miliyan biyu sun rasa rayukansu a cikinsa. A cewar Dr. Abdel Aziz, ƙwararre jami'i a cibiyar nazarce-nazarcen Afrika da ke da mazauninta a birnin Khartoum, ko shakka babu ɓallewar kudanci zai kawo cikas ga Arewaci.

Ya ce: "Ko shakka babu raba ƙasar gida zai janyo koma bayan tattalin arziƙi. Saboda cewa kenan za a amshe kashi ɗaya bisa huɗu na filayen Sudan da kuma dukkan arziƙinta na ƙarkashinsa da aka gano da kuma wanda har yanzu ba kai ga gano shi ba. Hakan na nufin rage yawan mazauna da kusan kashi ɗaya bisa huɗu, wanda bangare na masu ƙarfin aiki. Kuma sanin kowa ne cewa ci- gaban kasa yana ya dogara akan arzikinta na ƙarƙashin ƙasa da kuma ɓangaren al'umarta masu ƙarfin aiki."

Madatsar ruwan MeroweHoto: AP

Ko da yake rahotannin da bankin duniya ya fitar daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2008 sun nunar da cewa ba da arziƙin man fetur ne kaɗai Sudan ke dogaro ba, a cewar Abda Yahia Abdul Rahman Al Mahdi ɓangarorin biyu za su fuskanci babbar ƙalubale saboda cewa ƙasar ta Sudan ta fi mai da hanakali ne ga man fetur tare da yin watsi da aikin noma -abin da janyo zaman kashe wando tsakanin matsa a manyan birane.

Dogaro akan juna

A don haka gwamnatin Sudan za ta buƙaci gina sabbin madatsun ruwa a baya ga madatsar ruwan Merowe domin bunƙasa aikin noma. Kuma tuni masu zuba jari daga ƙetare suka nuna sha'awar shiga wannan aiki.To amma ga baki ɗaya dai ana bayyana shakku game da sakamakon zaɓen raba gardamar. Dalili kenan da ya sa kuɗin Pound na ƙasar ta Sudan ya faɗi warwas gabanin gudanar da zaɓen- abin da John Ashworth mai sa ido akan al'amuran ƙasar ta Sudan ya ce zai kawo cikas ga yanayin zuba jari. Saboda cewa har yanzu arewacin Sudan ba ta hange kyakyawar makoma sakamakon yaƙin da ake yi a yankin Darfur da kuma barazanar ƙara rincaɓewar rikice-rikicen da ake fama da su a yankin kudancin Kordafan da Abyei da Blue Nile da kuma gabashin ƙasar.

Mawallafiya: Lina Hoffman/ Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal