Barazanar ɗaukar matakin soji a kan Siriya
August 29, 2013Talla
Ƙasashen yamma na barazanar ɗaukar matakin soji kan Siriya ko ba tare da amincewar Majalisar Ɗinkin Duniya ba, kasancewar ƙasashen Rasha da China da ke goyon bayan Siriyar ka iya ɗarewa kan kujerar na ƙi. Wannan lamari dai na ɗaukar sabon salo domin al'ummar ƙasa da ƙasa ba ta so a maimaita irin abin da ya faru a Iraƙi kimanin shekaru 10 da suka gabata.
A ƙasa mun yi muku tanadin rahotannin da muka shirya kan wannan rikici na Siriya.