Barazanar aukuwar ambaliya a China
August 8, 2012
Talla
Wata guguwar da ake kira da sunnan Typhon Haikui wacce ta ke tafe da iska haɗe da ruwan sama mai ƙarfin gaske na shirin yin toroƙo a yankin gabasahin China inda jama#a suke cikin zaman ɗar ɗar.Guguwar wacce ta rastsa a yankin Zejang da ke a kudanci ,wadda ke da gudun kilomita 150 a ko wace awa guda.
Tuni da ta share wasu gidaje da dama tare da katse wutar lantarki a wasu ƙayuka kusan guda ɗari.A cikin watan Yuli na shekarar bara ruwan sama da aka riƙa shatatawa kamar da bakin ƙwarya a ƙasar ta China; wanda ba a taba yin irin su ba a cikin shekaru 60 ,sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 79 a birnin Bejin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu