1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona na barazanar haddasa yunwa a duniya

Muhammad Bello MNA
April 22, 2020

Sashen bunkasa samuwar abinci a duniya ya sanar a wani rahotonsa cewar, kasashen duniya tara za su fuskanci yunwa matsawar ba su maida hankali kan shawo bazuwar annobar Coronavirus ba.

Simbabwe Dürre Maisfeld
Hoto: picture alliance/Photoshot

A rahoton na Hukumar Abinci ta Duniya wato WFP, bayanai ne suka fito karara na cewar, labudda in har wadannan kasashe guda tara da suka hada da Najeriya ba su yi namijin kokari wajen dakile bazuwar annobar ta Covid-19 ba, to kuwa mummunar yunwa za ta sarki jama'arsu.

Hukumar ta kara cewar lallai kasashen duniya su farka sannan su yi abin da ya dace kuma kan lokaci, bisa abin da ke fuskantar duniya din, mai jibi da annobar ta Corona.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tuni wannan annoba ta Covid-19 ta yi ragaraga da tattalin arzikin da daman kasashen duniya kawo yanzu.

Dogayen layuka don sayen abinci saboda Corona ya zama ruwan dare kamar nan a Afirka ta KuduHoto: AFP/M. Longari

Bayan dai Najeriya da ke cikin lissafin Majalisar ta Dinkin Duniya kan cewar jama'ar su za su fuskanci matsananciyar yunwa, akwai Yemen, Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Haiti da Sudan da kuma Venezuela. Sauran su ne Sudan ta Kudu sai Afghanistan.

Dakta Ross Maxwell Gidado, mataimakiyar Darakta ce a hukumar fasahar samar da irin gona na zamani, kuma jami'a ce a cibiyar Open Forum on Agricultural Bio-Technology ta nahiyar Afirka a Najeriyar da ta ce.

"Zan iya yarda da maganar Majalisar Dinkin Duniya, domin tun ma kafin bullar annobar Corona, da ma a Najeriya da ma nahiyar Afirka muna da matsalar wadatar abinci da kuma ma cimakar da suka dace. Don haka bullar annobar Corona na kara tabarbara al'amura ne kawai. Kuma koda a yanzu ma maganar da ake yi, akwai mace-mace ma su

Wannan rahoto dai na Hukumar Abinci ta Duniya hakika ya dada tada hankulan jama'a, musamman ma a Najeriya.

A fadin duniya dai yanzu,Cutar ta Corona ta kashe jamaa sama da dubu dari da sabain da biyar,sannan kuma sama da miliyan 2 da rabi na dauke da ita.