Bala'i
Barazanar karancin abinci a nahiyar Afirka
September 6, 2018Talla
Kwararrun sun ce nau'in tsutsar nan zunkudau da ta samo asali daga kasashen Latin Amirka da kuma aka gano yaduwarta a kasashen Afirka a shekara ta 2016, yanzu haka na yaduwa kamar wutar daji inda tuni aka gano ta a kasashe 44 daga cikin kasashen nahiyar Afirka sabanin kasashe 28 a shekarar da ta gabata.
Kwararrun sun kiyasta cewa mutane sama da miliyan 300 ne ka iya fuskantar barazanar karancin abinci a shekarar ta bana a sakamakon wannan tsutsa da sauran kwarin wanda babu wani nau'i na shuka da ba sa far ma wa.