Barazanar Koriya ta Arewa kan Amirka
April 14, 2017Talla
Kasar Koriya ta arewa, ta yi barazanar ragargaza Amirka muddin Amirkar ta kai mata hari, da ta hasaso alamun faruwar hakan.
Rundunar sojin kasar ta yi barazanar cikin wani sakon kashedin ta a wannan Juma'ar, ta yi gargadin ne saboda bayanan da ke nunin cewa Amirka na shirin afkawa mata a fargabar ta na yiwuwar Koriyar ta aiwatar da gwajin makamin Nukiliyar ta karo na shidda.
Wani babban jami'in sojan kasar ya ce muddin Amirka ta yi abin da ya danganta shi da garaje, babu wani abin da zai hana su daukar mummunan matakin martani kan Amirkar.