Mayakan jihadi na barazana ga tsaron Burkina Faso
February 21, 2023Alkaluma na wadanda suka mutu a sakamakon harin ta'addanci da aka kai kan rundunar sojin kasar Burkina Faso ya haura zuwa hamsin da daya, bayan da aka gano karin gawarwaki arba'in da uku a ranar Litinin din da ta gabata. Mayakan masu da'awar jihadi, ake zargi sun kai wa rundunar sojin hari irin na kwanton bauna a wani yanki mai suna Oudalan, kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar ta sheda.
Tun dai a makon jiya aka kai harin a daidai lokacin da gwamnatin Burkina Fason, ta tsaya kai da fata na ganin lallai sai sojojin Faransa kimanin dari hudu da suka yi saura a kasar sun fice. Masana tsaro a na su bangaren na ganin cewa, sabanin da aka samu a tsakanin Faransa da kasar ne ya kara bai wa mayakan masu da'awar jihadin damar cin karensu ba babbaka, wanda shi ke kara tasiri a munanan hare-haren da kasar ke fuskanta a yanzu.