Barazanar Burundi bayan zargin cin zarfi
September 14, 2018Kasar Burundi ta yi barazanar fita daga Hukumar Kare Hakkin Dan-Adam ta Majalisar Dinkin Duniya idan " siyasa ta ci gaba da tasiri a cikinta". Wani babban jami'in fadar shugaban Burundi ne ya yi wannan shelar, a lokacin da wata tawagar gwamnatin kasar ta isa Geneva domin gabatar da rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin siyasa da Burundi ta yi fama da shi.
Wannan rahoto ya bayyana cewa an ci zarafin al'umma a Burundi a shekara ta 2017 da 2018 sakamakon kalaman nuna kyama da Shugaba Pierre Nkurunziza ya yi ta yayatawa. Masu bincike na duniya sun dora alhakin tauye hakkin bil Adam a kan jami'an tsaro da kuma mayakan sa kai na reshen matasa na jam'iyar shugaban kasa. Sai dai hukumomin Burundi sun yi watsi da wannan rahoto, suna mai cewa babu kamshin gaskiya a cikinsa
Tun Shekara da ta wuce ne, hukumomin duniya suka aika da masana uku don gudanar da bincike tare da hadin gwiwar gwamnati Burundi domin a gano wadanda suka aikata manyan laifuka a kasar da nufin gurfanar da su gaban kuliya.