1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar rugujewar jam'iyyar PDP

January 2, 2014

A kokarin kashe wutar rikicin dake barazana ga kujerar mataimakin shugaban tarrayar Najeriya, fadar gwamantin kasar ta karyata zargin rushewar PDP a jihohin dake sashen arewa maso yammaci.

Hoto: AFP/Getty Images

Rahotanni na baya-bayanna nan dai na nuni da cewa jam'iyyar PDP dake mulki a Tarayyar Najeriyar tun bayan da kasar ta koma kan turbar dimokaradiyya a shekara ta 1999, na fuskantar barazanar rushewa a mafiya yawan jihohin na sashen arewa maso yammaci wanda kuma mataimakin shugaban kasar Alhaji Namadi Sambo ke jagoranta.

Cikin dan kankanin lokaci dai iska ta kada kuma ba akai ga ko'ina ba zumbutu na kaza ke neman fitowa fili a siyasar Tarrayar Najeriyar dake sauyin launi da salo, da kuma yanzu haka ke neman fitowa da raunin mataimakin shugaban kasar Alhaji Namadi Sambo.

Kama daga Sokoto ya zuwa Kano dama kadunan da yake takama da ita dai, daruruwa na 'ya'yan PDP ne suka kai ga adabo da uwar lemar da ta fuskanci barazana mafi girma sannan kuma ke neman girgiza ita kanta kujerar mataimakin shugaban kasar da ya share tsawon kusan mako guda a cikin jihar ta Kadunan, ya kuma yi kokari na nunacewa har yanzu fa lemar na iya magani da marka marka.

Hoto: DW/U.Abubakar Idris

Guguwar sauyi a jihohin arewa maso yamma.

Kafin sabuwar guguwar sauyin dai jiha daya tilo a cikin yankin dake da jihohi har guda bakwai ke zaman karkashin ikon jamiyyar APC , to sai dai kuma sabon rikicin ya kai ga ficewar karin jihohin Kano da Sakkwato da kusan kwai da kwarkwata na 'ya'yansu suka ce a kai ga kasuwa ga makomar lemar. Haka can ma a Kadunan dai APC tace ta karbi sababbin 'ya'ya har 1,200 a karamar hukumar da Sambon ya fito, abun kuma da ya fara dora tunani na rashin tabbas a bisa tasirin mataimakin shugaban kasar dake zaman mutun na biyu mafi karfin iko a cikin jamiyyar da kuma ke fuskantar barazana mafi girma. To sai dai kuma a nasa martanin mataimakin shugaban kasar ta hannun kakakinsa Umar Sani yace PDP na nan daram dam kuma ma tana karin karfi a daukacin yankin duk da ficewar 'ya'yan da yace basu da tasirin hanata cigaba da rawa irin ta hantsi a cikinsa.

Jagoran jam'iyyar adawa ta APC Janar Muhammad Buhari murabus.Hoto: DW/N. Zango

Barazanar kwace kujerar Namadi.

Farfaganda ta siyasa ko kuma kokari na karin rikici dai, tuni juya akalar ta arewa maso yamman ke neman sauya salo a cikin rikicin na jamiyyar PDP inda 'yan jamiyyar dake arewa maso gabas ke neman maye Sambon da ministan babban birnin tarraya na Abuja a lokutan zaben shugaban kasar na 2015. Ra'ayi dai yazo daya a kusan dukkanin shugabannin PDP na arewa maso gabas na neman kawo karshen Sambon da suke zargi da kasa hana 'yan siyasar yankin nasa bore ga gwamnatin jam'iyyar ta kasa tare da mai da kujerar ya zuwa arewa maso gabas da ake yiwa kallon yankin da har yanzu PDP ke da dan sauran karfi a ciki.

To sai dai kuma a fadar Garba Umar Kyari dake zaman masani ga siyasar kasar ta Najeriya, guguwar sauyin ta arewa maso yamma dai na kama da gobara daga teku Allah kadai ke iya maganin ta ba masu siyasar ta arewa ba.

Abun jira a gani dai na zaman mafita a cikin sabon rikicin da ke iya kara gara kawuna a cikin PDP da ta shiga shekarar yakin neman zabe da mugun dafi na harbi na adawa a jikinta.

Mawallafa: Ubale Musa / Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal