1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin sauke Saraki a majalisa

Uwais Abubakar Idris YB
August 2, 2018

Takaddama ta kunno kai a majalisar dokokin Najeriya, inda ‘yan jam'iyyar PDP a majalisar wakilai suka yi alkawarin ci gaba da kwanan zaune a majalisa, don kar a tsige shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki.

Nigeria Bukola Saraki
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Wannan barazana dai ta sanya samun sauyi a majalisar tarayyar inda aka ga karin jami'an tsaro da ma sanya sarka aka garkame kofofin majalisar duk a kokari na kauce wa yunkuri tsige shugaban majalisar.

Domin ‘yan jamiyyar PDP da ke majalisar wakilan Najeriya sun ce ba za su bari a yi masu sakiyar da ba ruwa ba bisa abin da suka kira yunkuri na tsige shugaban majalisar dattawan Najeriyar Sanata Bukola Saraki. Timothy Simon na cikin wadanda suka kwana suna gadin majalisar. Ga mafi yawan 'ya'yan jam'iyyar APC na ganin ba fa za ta sabu ba suna da rinjaye amma kuma wasu su jagorancesu. To sai dai ga Hon Nasiru Sule ya ce  ba za su yarda ba.

Da dama na ganin akwai jikakka tsakanin Saraki da BuhariHoto: DW

A yayin da hatta ‘yan jam'iyyar PDP ke bayyana amanna na yiwuwar sake bude majalisar kafin lokacin hutun watani biyu da suke ciki, da alamun za a sha ‘yan kallo a kan wannan batu. Wannan ne dai karon farko da jam'iyyar adawa marasa rinjaye ke shugabancin majalisar dattawan kasar.