Barazanar Sudan ga Sudan ta kudu
April 19, 2012Shugaba Omar Hasan al-Bashir na Sudan ya yi barazanar hamɓarar da takwaran aikinsa na Sudan ta kudu, bisa dalilan da ya danganta da neman ceto al'umar ƙasar daga rikicin kan iyaka na ƙasashen biyu da ke maƙobtaka da juna. Al-Bashir ya bayyana cewar Salva Kir da ke shugabantar Sudan ta kudu tun bayyan da ta zama ƙasa mai cin gashin kanta a watan julin bara, wani ƙwaro ne da ya kamata a kawar daga karagar mulki.
Shi dai salva Kir, tsohon shugaban ƙungiyar tawaye na ta SPLM ne, da ta yi ta takun saƙa da Gwamnatin tsohuwar haɗaɗɗiyar Sudan, sakamakon zarginta da mayar da 'yan kudancin ƙasar saniyar ware. Ƙasashen biyu na taƙaddama ne da juna game da wani yankin kan iyaka mai arzikin man fetur.Faɗace faɗace sun tsananta a makwanin baya-bayannan tsakanin Sudan da kuma Sudan ta kudu.
A halin yanzu dai ƙasar Sudan ta kudu ta mamaye yankin Heglig mai arzikin man fetur kuma mallakin ƙasar Sudan. Ƙasashen duniya daban daban sun yi kira ga ɓangarorin biyu da ke gaba da juna, da kai hankali nesa tare da komawa kan teburin shawarwari domin warware rikicin na kan iyaka tsakanin Sudan da kuma Sudan ta kudu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu