1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Barazanar ta'addanci:Yan sandan Munich na sintiri a Allianz

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 30, 2024

'Yan sandan sunsanar da kamfanin dillancin labaran Jamus DPA cewa wani da ake kyautata zaton yana da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ne ya wallafa wasu hotunan wuraren da suke hari, ciki har da Allianz Arena

Hoto: RONALD WITTEK/EPA

Rundunar 'yan sandan birnin Munich a nan Jamus ta kara yawan jami'anta a kewayen harabar filin wasan Bayern Munich wato Allianz Arena, tun gabanin karawar da kungiyar da babbar abokiyar hamayyarta Borussia Dortmund, biyo bayan bayanan sirri da ta samu na barazanar harin ta'addanci.

Karin bayani:Jamus: Sumamen 'yan sandan a Kolon da Berlin

Mai magana da yawun rundunar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA cewa wani da ake kyautata zaton yana da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ne ya wallafa wasu hotunan wuraren da suke hari, ciki har da Allianz Arena, dalili kenan da ya sanya suka tsaurara bincike da matakan tsaro a wurin.

Karin bayani:Masallatai a Jamus na fuskantar barazana

A baya bayan dai IS ta dauki alhakin harin da aka kai wani gidan rawa a birnin Moscow na Rasha ranar 22 ga wannan wata na Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 144.