1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asibitoci na cika da masu corona a Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
November 18, 2021

Mahukuntan Jamus za su takaita wasu harkoki na walwalar wadanda ba su yi allurar rigakafi ba, a yankunan da asibitoci ke cika da masu corona.

Vor PK der Ministerpräsidentenkonferenz mit der Bundeskanzlerin
Hoto: dpa

Shugabanni na tarayya da jihohin kasar 16, a wani taron da suka gudanar a yau Alhamis suka cimma wannan matsayi na ba-sani-ba- sabo, wanda ke zama martani ga barazanar sake ta'azzarar cutar corona a karo na hudu a Jamus.

Daga yanzu sai wanda ke da shaidar yin allura ko kuma bai jima da warkewa daga cutar ba ne, zai iya shiga wuraren wasanni ko cin abinci da makamantansu a yankuna da cutar ta fi kamari.

Saxony, ita ce jihar da ta fi kowacce shiga cikin wadi-na-tsaka-mai wuya na yaduwar cutar coronar a karo na hudu, tuni kuma ta fara la'akari da kafa dokar kulle tare da rufe mafi yawan wuraren shakatawa.

Jihar ce dai aka fi samun karancin masu allurar rigakafi a yankin gabashin Jamus, kuma ke da mafi yawan wadanda suka kamu da COVID 19.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW