Barazanar yunwa a wasu kasashen Afirka
April 11, 2017Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa a shekarar bana akwai barazanar samun mace-mace masu dinbin yawa a kasashen yankin kahon Afirka da Najeriya da Yemen sanadiyyar yunwar wacce matsalar fari dama tashe tashen hankula da ake fuskanta a wadannan kasashe suka haddasa.
Kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya Adrian Edwards ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira a wannan talata a birnin Geneva. Majalisa Dinkin Duniya ta ce tana fargabar yunwar da za a fuskanta a shekarar ta bana a kasashen yankin kahon Afirka ta fi wacce aka fuskanta a shekara ta 2011 da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 260 tsanani.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi shelar neman agajin kudi na kusan biliyan hudu da rabi na Dalar Amirka nan zuwa watan Yuli domin kai kayan abinci da magunguna a kasashen guda hudu inda mutane miliyan 20 ke fuskantar barazanar ko dai ta yunwa ko kuma ta karancin abinci mai gina jiki.