Barcelona ta rattaba hannu da DRC kan tallata yawon bude
July 17, 2025
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu ganin daftarin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Kinshasa da Barcelona, wanda Kwango za ta rinka biyan kungiyar Yuro miliyan 11.5 a duk shekara har tsawon shekaru hudu, domin bunkasa fannin yawon bude ido na kasar a rigunan 'yan wasan kungiyar.
Karin bayani:Ruwanda: Ko karshen rikici da Kwango yazo?
Ministan Wasanni na DRC Didier Budimbu ya shaida wa Reuters cewa baya ga Barcelona, kungiyoyin kwallon kafar irin su AC Milan da AS Monaco sun bukaci kulla yarjejeniya na kimanin Yuro miliyan 1.6 a duk kakar wasanni da AS Monaco da kuma na Yuro miliyan 14 a duk kakar wasanni da AC Milan.
Karin bayani:Barcelona ta isa Paris don cinikin Neymar
A watan Fabrairun 2025, ministar harkokin wajen Kwango Therese Kayikwamba Wagner ta bukaci kungiyoyin kwallon kafar Arsenal da Bayern Munich da kuma Paris St Germain da su kawo karshen tallata Ruwanda a rigunan 'yan wasansu, sakamakon rawar da take takawa da rikicin DRC da M23.