1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barcelona ta yi raga-raga da Real Madrid

Suleiman Babayo AH
March 21, 2022

A Spain, a wasan lig na La Liga, aka yi karawa da ake kira El Clasico tsakanin kungiyar Real Madrid da ta karbi bakubcin Barcelona, kuma kungiyar ta Barcelona ta yi raga-raga da Real Madrid da ci 4 da nema,

Fußball Real Madrid - FC Barcelona 0:4
Hoto: NurPhoto/IMAGO

 an kara wannan wasa a filin wasa na Santiago Bernabéu Stadium da ke daukan mutane 81,000, kuma milyoyon 'yan kallo daga kasashe suka kalli wannan wasa mai tasiri. Sannan Espanyol ta doke Mallorca 1 mai ban haushi, kana Atletico Madrid ta yi Rayo Vallecano gida ta lallasa ta 1 da nema, yayin Sevilla da Real Sociedad suka tashi babau wadda ta jefa kwallo a raga.

A teburin na la Liga adda tsarin yake:

Hoto: Marca/IMAGO

1 Real Madrid         maki    66
2 Sevilla                             57
3 Barcelona                       54
4 Atlétic                              54
5 Betis                               50 

A wasan Premier League na Ingila, Arsenal ta bi Aston Villa ta doke ta 1 da nema. Sannan Tottenham ta doke West Ham 3 da 1

A wasannin Bundesliga na Jamus, kungiyar Mainz ta doke Arminia 4 da nema, haka ita ma Bayern Munich ta doke Union Berlin 4 da nema, sannan Hertha Berlin ta doke Hofffenheim 3 da nema, yayin da Leverkusen ta bi Wolfsburg gida ta doke ta 2 da nema. Ana ta bangaren kungiyar Greuther Fuerth ta tashi babu jefa kwallo a raga da Freiburg. Kuma wasan da kungiyar Stuttgart ta doke Augsburg 3 da 2 muka kawo muku kai tsaye daga nan Sashen Hausa na DW, inda na gabatar da sharhin tare da Ramatu Garba Baba.

A teburin Bundesliga ga shima yadda tsarin yake

Hoto: Teresa Kröger/Kirchner-Media/IMAGO

1 Bayern München            maki    63
2 Dortmund                                   57
3 Leverkusen                                48
4 Leipzig                                       45
5 Freiburg                                     45

A kasar Amirka lamuran wasannin na ci gaba da farfadowa bayan matakan annobar cutar coronavirus da duniya ta fuskanta.