1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barrow ya nada mataimakiyar shugaban kasa

Gazali Abdou Tasawa
January 24, 2017

Shugaban Gambiya Adama Barrow ya nada Fatoumata Jallow a matsayin mataimakiyar shugaban kasa.

Adama Barrow Präsident von Gambia
Hoto: Getty Images/AFP

A yammacin jiya Litinin ne dai sabon shugaban shugaban na Gambiya Adama Barrow ya nada Fatoumata Jallow a matsayin mataimakiyar shugaban kasa kamar yadda Halifa Sallah kakakin shugaba Barrow din ne ya shaida wa manema labarai. Mrs. Jallow dai 'yar fafutikar kare hakkin mata ce kana tsohuwar ma'aikaciyar Majalisar Dinkin Duniya sannan kuma a baya ta riki mukamin ministan kiwon lafiya daga shekara ta 1994 zuwa 2017 a tsohuwar gwamnatin Jammeh. 

Fatoumata Jallow ta kasance daya daga cikin mambobin kawancan da ya goyi bayan takarar Adama Barrow a zaben ranar daya ga watan Disemba shekarar bara. A baya-bayan nan wasu kalamai da ta furta na neman ganin an gurfanar da Shugaba Jammeh a gaban kuliya sun haifar da cece-kuce tsakanin jam'iyyun kawancan wadanda akasarinsu ke bukatar ganin an warware matsalolin kasar ta Gambiya ta hanyar kafa kwamitin tantance gaskiya da kuma sasanta 'yan kasar.