SiyasaBelgium
An rantsar da sabon firaministan Beljiyam
February 3, 2025
Talla
Bart De Wever ya sha rantsuwa kama aiki a gaban sarki Philippe a fadar sarkin tare da mambobin gwamnatinsa 14.
Bart mai shekaru 54 wanda ya kwashe shekaru 12 a matsayin magajin gari na Anwert ta arewa, shi ne dan awaren Flemish na farko da ya karbi shugabancin gwamnatin tarayya a Beljiyam
Kusan watanni takwas bayan gudanar da zabukan ‘yan majalisu, wanda jam'iyyarsa ta N-VA ta samu nasara a Flanders,
kuma zai gudanar da mulkin tare da jam'iyyu hudu na kawance.