Barzani ya bukaci majalisa ta warware rikicin PKK
November 5, 2011Shugaban kurdawan Iraki Massud Barzani, ya nuna adawa da matakin soji da Turkiyya ta ɗauka domin yaƙar kurdawa 'yan adawa dake yankin arewacin Iraki, kasancewar hakan zai haifar da matsalar rashin samun mafitar din-din-din a wannan rikici. Tun a ranar alhamis ne Barzani ya isa birnin Ankara domin tattaunawa da magabatan Turkiyya dangane da ci gaban yaƙar kurdawa 'yan fafutukar neman 'yanci na ƙungiyar PKK da sojojin gwamnati ke yi. Shugaban kurdawan Irakin yace, matakin soji ba shine mafitaba, a zauren majalisar Turkiyyan ya dace ayi mahawarar kawo karshen wannan takaddama. Tun a watan daya gabata ne dai, sojojin Turkiyya suka kutsa yankin arewacin Irakin da hare-hare akan kurdawa 'yan adawan, harin dake zama ramuwar gayya bayan kurdawan sun kai harin daya kashe sojojin kasar guda 24 a garin Cukurka dake kusa da kan iyakar Iraƙi. Kashe sojoji 24 ɗin dai ya kasance mafi munin asarar da gwamnatin Turkiyyan ta yi, tun daga shekara ta 1993. Tuni dai Priminista Recep Tayyip Erdorgan na Turkiyyan ya bukaci gwamnatin Barzani ta taka rawa wajen yaƙar kurdawan na ƙungiyar PKK.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman