1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta kama shugaban Siriya

Abdoulaye Mamane Amadou
March 8, 2021

Shugaban Siriya Bashar al-Assad da mai dakinsa Asma, sun kamu da cutar corona bayan da aka yi masu wani gwajin cutar na gagawa don tantance lafiyar jikinsu.

Syrien Bashar Al-Assad 1999
Hoto: Getty Images/AFP/R. Moghrabi

Rahotanni sun ce shugaban da mai dakinsa sun yi gwajin ne bayan da suka soma jin wasu alamomi a jikinsu, sai dai fadar shugaban kasar ta ce Bashar al-Assad da mai dakinsa suna nan cikin koshin lafiya.

Sai dai shugaban zai ci gaba da aiki a gida a yayin da yake zaman killace kansa na tsawon makwanni biyu zuwa uku a cewar fadar shugaban kasar.