1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya tana cikin katutun bashi

Ubale Musa SB/MAB
April 19, 2023

Barazana mai girma ga makomar kaddarori na gwamnatin Najeriya inda hukumar kula da lamunin kasar ta ce Najeriya ta fara nuna alamu na gazawa bisa biyan bashi na kasar Sin/Chaina da ke wuyanta.

Nigeria Zug der Nigerian Railway Corporation
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

 

Kama daga layin dogo zuwa wutar lantarki gami da uwa uba tashoshi na jirage na sama dai, kasar Chaina/Sin tana zaman ta kan gaba a kokari na sake mai da tsohuwa yarinya a cikin Najeriya. Kuma ya zuwa watan Satumban da ya shude, kaso sama da 80 cikin 100 na basuka na kasashen waje da ke kan Najeirya sun fito ne daga Sin.

Karin Bayani: Bashi ya yi wa Najeriya katutu

To sai dai kuma a wani abin da ke dada nuna alamu na damuwa a halin yanzu, hukumar kula da basukan kasar DMO ta ce Najeriya ta fara nuna alamun rawar kafa wajen biyan kudin ruwa na basukan da aka kiyasta sun haura dalar Amurka miliyan dubu Hudu. Harkar sufurin jirage na kasa da kasar Sin ta taka rawa mai girma dai alal ga misali ta gaza kai wa ga biya na bukata na basukan da ke ta karuwa a halin yanzu.

Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

A yayin da alal ga misali jiragen kasa suka iya tara abin da ya kai Naira Miliyan Dubu 11 da sunan kudin shiga na dakon kaya da mutane a shekaru biyu baya, uwar kudi da ma ruwan da kasar Sin ke fatan ta gani a shekaru dai sun kai Naira Miliyan Dubu 41 adadin da ya nunka har kusan gida uku na kudin shigar a jiragen kasa.

Ya zuwa yanzu dai Najeriya tana biyan sama da kaso 96 cikin 100 na kudin shigar kasar wajen biyan kudin ruwa da kuma uwar bashin da ke ta karuwa cikin kasar. Akwai dai tsoron yiwuwar karbe kaddarorin Najeriya a bangaren 'yan Chaina da ke dada neman hanyar mamaye tattalin arziki na kasashen duniya. Chaina dai alal ga misali ta yi nasarar karbe wata tashar jiragen ruwa can a kasar Sri Lanka, ko bayan barazanar karbe wani kamfanin wuta a kasar Zambiya da ke yankin kudancin Afirka.