1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dan adawa ya lashe zaben shugaban kasar Senegal

Suleiman Babayo AH
March 25, 2024

Bayan kirga galibin kuri'u a zaben shugaban kasar, dan adawa Bassirou Diomaye Faye ya lashe zaben kuma tuni babban wanda ya kalubalance shi ya mika wuya.

Senegal | Bassirou Diomaye Faye wanda ya lashe zaben shugaban kasa
Bassirou Diomaye Faye wanda ya lashe zaben shugaban kasar SenegalHoto: SEYLLOU/AFP

Dan adawa a kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya lashe zaben shugaban kasar da gudanar a wannan Lahadi da ta gabata, inda yake da kashi 53 da doriya, cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da Amadou Ba dan takarar gungun jam'iyyun gwamnati yake da kashi 36 cikin 100, a cewar sakamakon hukumar zabe da kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito.

Hukumar zaben ta ce tuni ta kammala kirga kashi 90 cikin 100 na kuri'un. Shi kansa Shugaba Macky Sall mai barin gado na kasar ta Senegal ya taya dan adawan Bassirou Diomaye Faye murnar lashe zaben tare da cewa tsarin dimukaradiyya ya karfafa a kasar ta Senegal da ke yankin yammacin Afirka.

Shi kansa dan takara na bangaren gwamnati Amadou Ba ya mika wuya inda ya taya sabon zababben shugaban kasar murnar lashe.