1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bata canja zane ba game da makomar 'yan matan Chibok

Usman ShehuJune 20, 2014

Har yanzu akwai 'yan mata 276 a hannun Boko Haram, a cewar kwamitin da gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kafa da nufin binciko batar 'yan matan Chibok ya tabbatar a rahotonsa.

Nigeria Protest Boko Haram Entführung 26.5.2014
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Rahoton dai na zaman raba gardama cikin kasar ta Najeriya inda kawuna suke rabe tsakanin ko lalle an sace 'yan mata 'yan makaranta na Chibok sama da dari biyu, cikin watan Afrilu ko kuma ma an mai da karatun na siyasa a tsakanin gwamnatin jihar da ke zaman ta adawa da kuma abokan takunta na Tarrayar kasar ta Najeriya, da ke jagorantar tsaro a yankin baki daya.

'Yan mata 276 ne dai a fadar shugaban kwamitin Janar Ibrahim Sabo, har yanzu ke a hannun Boko Haram, a yayin kuma da wasu 57 suka yi nasarar kubucewa cikin yanayi daban-daban da kwamitin ya bayyana yayin mika rahoton nasa.

A cikin watan Mayu dai mahukuntan na Abuja suka kai ga nadin kwamitin da nufin tantance aya a cikin tsakuwa, bayan kwan gaba-kwan-bayar da aka rika fuskanta a bangarori daban-daban da ke da ruwa da tsaki da yakin cikin kasar na ta'addanci.

Janar Ibrahim Sabo dai na zaman shugaban kwamitin da ya ce ya je har garin Chibok ya kuma gana da kusan kowa da nufin sanin abun da ke kasa game da batun satar yaran inda ya kara da cewa.

Hoto: picture-alliance/AP

“Saboda maganganu daban-daban da aka yi shi ya sa muka zo muka hada kan shugabanni. An saci yaran nan ba kage ba ne, 276 ba a gano ba, amma an samu 57. Ba zan bayyana maka ko mun bada shawarar sulhu ba, haka kuma ba zan fada maka ko sakaci aka yi, ko kuma abun da ya faru a garin na Chibok na zaman na tsautsayi, saboda mun sa komai cikin rahotonmu. Amma dai muna da imanin aiwatar da rahoton na iya kaiwa ga tabbatar da gano yaran.”

To sai dai kuma a fadar shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan da ya karbi rahoton a gaban daukacin hafsoshin tsaron kasar, ya yi kurari har yanzu akwai sauran fata na tabbatar da gano 'yan matan, da ma kila kaiwa ga ganin baya na kungiyar da ke nuna alamar wucewa da sanin 'yan mulkin kasar ta Najeriya.

“Dole ne mu murkushe wannan Boko Haram, dole ne mu kawo karshen kalubalen da ke a gabanmu. Bari in kara bada tabbaci ga al'ummar Chibok, musamman ma iyayen yaran nan cewar, muna jin ciwon su, kuma muna cikin yanayi irin nasu. Musamman ma ni da ke zaman shugaban kasa, da ke da bayanai daban-daban. Amma dai ina basu tabbacin cewar gwamnati za ta ci gaba da kokarinta har sai an gano yaran nan. Dole ne mu gano 'yan matan nan, iyayen su kara hakuri damu kawai”

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani