Bata kashi tsakanin rundunar yan sanda da yan kungiyar Alka´ida a Saudiyya
September 6, 2005A kasar saudiyya a na ci gaba da bata kashi, tsakanin jami´an tsaro, da yan kugiyyar Alqa´ida a birnin Damman, dake gabancin kasar.
Tun ranar lahadin da ta wuce, yan sanda su ka yi kofar raggo ga yan Alqa´idan, a wani gida da ke birnin Damman.
A ranar farko, rahotani daga opishin ministan cikin gida na Saudiyya ,sun bayana cewa,harbe-harbe tsakanin bangarorin 2 sun hadasa mutuwar mutane 2, daga bangaren yan tawayen da kuma dan sanda guda.
Jami´an tsaro, sun ci gaba da farautar Karin wasu mutane da ake tuhuma, da hannu a cikin ayyukan ta´adanci, a Saudiyya kamin sun yi zobe ga gidan da ya taada´r su ka ja daga.
Kafofin sadarwa na kasar, na bayana cewa, mutane kimanin 10 kawai, a cikin wannan gida su ka faskari jami´an tsaron Sauddiya.
A yammacin jiya litinin, hukumomi sun bayyana Karin mutuwar yan Alqa´ida 3, da kuma da kuma yan sanda 2.
Sun kuma ce an ci gaba da harbe harbe, a wannan gida taskanin daren jiya zuwa sahiyar yau talata, saidai, ya zuwa yanzu, babu cikkaken bayyani, na karin yawan mutane da su ka mutu.
A jimilce daga fara wannan arangama, yau da kwanaki 3, da su ka wuce, ya zuwa yanzu, sakamakon wuci gadi, ya tabatar da mutane 7 su ka rasa rayuka, daga bangarorin 2.
Mazamna unguwar Al haram, da rikicin ke wakana, sun shiga wani hali na rudani.
Rahotani sun shaida cewa, da dama sun boye a gidajen su ,domin riga kafi ga illolin da battatun harssasai kan iya jawo masu.
Haka zalika, unguwar da ke daya, daga wuraren cunkosson kasuwanci ta kasance, sakai a halin da ake ciki.
Kasar Amurika,ta bada sanarwar rufe karamin opishin jikadancin ta, dake Dahran kussa da Damman, inda fadan ke wakana, don riga kafi.
Tun daga shekara ta 2003, kasar saudiyya ke fama da hare haren ta´adanci daga yan kungiyar Alqai´da da ke zargin hukumomin kasar, da zama yan amshin shatan Amurika.
A watan da ya gabata, jami´an tsaro, sun yi nasara bindige Saleh Al-Ufi, daya daga jagororin kungiyar Alqa´ida, a Saudiyya a cikin wani bata kashi ,da aka yi tsakanin rundunonin 2, a birnin Madina.
Saleh Al-Ufi, na daga jerin mutanen da Amurika ke nema ruwa jallo.
Bayan hawan sa karagar mulki, a watan da ya gabata, saban Sarkin mai ci yanzu, na Saudiyya, yayi kira ga daukacin yan kasar Saudiyya, da su gama karfi, domin yakar ta´adanci da ke bata suna da martabar wanann kasa mai tsarki.
Haka zalika, ya gayyaci yan ta´adar da su gane gaskya, su koma hanya, domin suma, su kawo ta su gudummuwa, a fadi ka tashin hukumomi na kyawttata rayuwar jama´a.