Batakashi tsakanin yan taliban da rundunar NATO
September 4, 2006Talla
A na ci gaba da gwabazawa tsakanin dakarun ƙasa da ƙasa na ƙungiyar tsaro ta NATO, da yan taliban a kudancin Afghanistan.
Tsakanin daren asabar zuwa lahadi, a ƙalla yan taliban 200 su ka rasa rayuka, da kuma sojoji 4 yan ƙasar Canada, na NATO, a bata kashin da ɓangarorin 2 su ka yi, a yankin Khandar.
A cikin artabon ne, wani jirgin sama yayi salla da kai, inda a nan take, sojojin Britania 14, su ka sheƙa lahira.
Tun bayan watan juli da ya wuce, wannan shine faɗa mafi muni, da ya haɗa ɓangarorin 2.
Wani mai magana da yawun yan taliban, ya ce su ne,ke da alhakin kakkaɓo jirgin Britania, da ya tarwatse, sannan babu ɗaya daga mayaƙan taliban da ya rasa rai, a cikin faɗan na jiya.