Batanci: Indiya na shan suka daga Musulmi
June 6, 2022Kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, na ci gaba da bayyana bacin ransu a kan wasu kalaman batanci ga Manzon Tsira da wata babbar jami'a ta jam'iyyar BJP da ke mulki a Indiya ta yi.
Tuni dai wasu kasashen na Larabawa suka ba da umurnin daina saye da ma amfani da kayayyakin da Indiyar ke sarrafawa wadanda ke a manya da kananan kantuna.
Haka ma kasashen sun yi kiran jakadun Indiya domin gabatar musu da korafi domin neman bayanai kan batancin da suka yi wa Annabi Muhammadu Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.
Hadaddiyar Daular Larabawa ce dai kasa ta baya-bayan nan da ta nuna fushinta, tana mai cewa hakan ya ci karo da kyakkyawar akida da dabi'u da ma kamala ta dan Adam.
Ita ma jami'ar Al-Azhar da ke a Masar, muhimmiyar cibiya ga Musulmi na duniya ta ce kalaman da kakakin jam'iyyar BJPn ta Indiya ta yi, ta'addanci ne da ke iya haddasa fitina a duniya.
Indiya dai ta sanar da dakatar da matar da ta yi wadannan kalamai na sabo.