1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun cin hanci da rashawa a Kenya na daukar sabon salo

Ibrahim SaniFebruary 2, 2006

Kiraye kiraye ga wasu jami´an gwamnati a Kenya na ci gaba da tsananta bisa zargi da ake musu da tafka almundahana

Kwana daya bayan murabus din ministan kudi na kasar ta Kenya, wato Mr David Mwiraria,ya zuwa yanzu kiraye kiraye naci gaba da yawaita ga wasu jami´an gwamnatin na suyi murabus daga mukamansu.

Kiraye kirayen sun yawaita ne kawai ga jami´an gwamnatin da ake zargi nada hannu a cikin almundahanar miliyoyin daloli da aka tafka a kasar.

A waje daya kuma wata majiya mai karfi daga ofishin shugaban kasar ta kenya, ta tabbatar da cewa tuni shugaba Mwai Kibaki ya umarci ragowar ministoci biyun da ake zargi nada hannu a cikin wannan almundahana da suyi murabus.

Wadannnan ministoci dai sun hadar da ministan makamashi, wato Kiraitu Murungi da kuma mataimakin shugaban kasar, wato Moody Awori.

Rahotanni dai sun nunar da cewa da cewa kiraye kirayen yin murabus din mutanen da ake zargi na da hannu a cikin wannan ta´asa , yafi tsanan ta ne daga bangaren kafafen yada labaru da jam´iyyun adawa da yan siyasa da kungiyoyi masu zaman kann su da kuma da yawa daga cikin talakawan kasar.

A misali wata malamar makaranta mai suna Margaret Opala dake da shekaru 55, ta tabbatar da cewa murabus din ministan kudin na nuni ne da cewa batu na cin hanci da rashawa a kasar ya kai wani hali na La´ula ha úla i.

Bisa hakan malamar ta tabbatar da cewa tana fata hakan, ka iya zama darasi ga yan kasar na kaucewa wannan mummunan dabi´a.

Rahotanni dai sun nunar da cewa Mr David Mwiraria na daga cikin sahun gaban manya manyan jami´an gwamnati da suka yi murabus a kasashen mu na nahiyar Africa , bisa zargi da ake musu da batu na cin hanci da rashawa.

Bayanai dai sun nunar da cewa hukumar yaki da aiyukan cin hanci da rashawa ta kasar ta Kenya na zargin Mr David Mwiraria ne tare da wasu ministoci biyu a hannu daya kuma da wani tsohon minista da hannu a cikin wannan almundahanar da aka tafka, ta biyan wasu miliyoyin daloli ga wasu kamfaninnika na jabu, bisa gudanar da aikin samar da ingantattun takardaun fasfo da kuma gudanar da bincike a kann gawarwaki.

Duk da cewa an dade ana tattauna wannan batu a fagen siyasar kasar, bai fito fili ba sai bayan da shugaban hukumar yaki da aiyukan cin hancin da rashawa, wato John Githongo ya tabbatar da cewa yana da ingantattun bayanai dake nuni da cewa akwai hannun wasu jami´an gwamnatin a cikin wannan almundahana da aka tafka.

Ya zuwa yanzu dai da yawa daga cikin masu fashin baki na ganin cewa saukar wadannan ministoci biyu daga mukaman su ka iya karfafawa mutanen kasar da kuma kasashen yamma gwiwa cewa akwai alamun gaskiya a cikin ikirarin da gwamnatin ta Kibaki keyi na cewa tana yaki da aiyukan cin hanci da rashawa a fadin kasar baki daya, kamar yadda take nunawa.