1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun gudun hijira ya mamaye ziyarar Merkel a Afirka

October 10, 2016

Shugabar gwamnati Jamus Angela Merkel ta gana da Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar wanda kasarsa ke zama daya cikin manyan hanyoyin 'yan gudun hijira a hanyar zuwa Turai.

Afrika Niger Ankunft Angela Merkel in Niamey
Shugaba Mahamadou Issoufou da Merkel ta Jamus a ziyararta NijarHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler


Ziyarar ta wuni daya da shugabar gwamnatin Jamus  Angela Merkel ta kawo a Birnin Niamey na zuwa ne a yayin da har yanzu wasu 'yan kasar ta Jamhuriyar Nijar ba su manta da radadin wasu hare-haren ta’addancin da suka shafi kasar ba, musamman ma na baya-bayan nan da aka kai a wani yankin kasar da ke iyaka da Mali inda wasu 'yan ta’adda suka hallaka sojan kasar su kimanin 22.

Batun yaki da ayyukan ta’adanci da maganar bakin haure ko batutuwan bunkasa karkara na daga cikin muhimman batutuwan da shugabannin kasashen biyu suka tattauna a tsawon wuni daya inda gwamnatin Jamus din ta kudiri aniyar taimaka wa Nijar ta fanonin karfafa wa jami’an tsaron kasar da horo da kayan aiki, uwa uba batun samar da wata cibiyar tallafa wa sojanta 650 da ke kasar Mali a karkashin inuwar MINUSMA wanda kuma tuni amincewar gwamnatin Nijar kan wannan matsayin ya tayar da hankalin wasu 'yan kasar wadanda ke cewa za a sake musu mulkin mallaka.

Ginin fadar gwamnatin NijarHoto: DW/M. Kanta

Bangarorin kasashen biyu dai sun cimma daidaito kan dafa wa Nijar da ke bukatar kudade sama da miliyan dubu daya na Euro don dakile matsalar bakin haure wanda aka kiyasta akalla mutum dubu 100 zuwa dubu 120 ne a wannan shekarar za su bi ta Nijar don zuwa Turai.

Daga shekarun 2015 zuwa 2016 kasar Jamus ta tallafa wa Nijar da Euro kimanin miliyan 62 a fannoni da dama kamar Ilimi da kiwon lafiya da tsarin decentralisation.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani