Batun zuba jari a Afirka ya dauki hankalin jaridun Jamus
April 27, 2018Za mu yaye kallabin shirin ne da sharhin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta dangane da rashin tasirin Jamus a kan harkokin zuba jari a kasashen Afrika. Sharhin mai taken "Alkawura babu cikawa" na sukar lamirin 'yan kasuwar Jamus na gindaya alkawura ba tare da cikawa ba.
Kungiyar hadin gwiwar 'yan kasuwar Afirka da ke nan Jamus, ta bayyana takaicinta dangane da manufofin gwamnatin Tarayya kan Afirka. An sanar da shekara ta 2017 da ta gabata a matsayin "shekarar Afirka" inda aka sanar da aiwatar da wasu shirye shirye muhimmai a kan nahiyar ciki har da hadin gwiwar bunkasa tattalin nahiyar ta hanyar zuba jari. Shugaban kungiyar 'yan kasuwar Stefan Liebing ya bayyana takaicinsa dangane da yadda Jamusawan ke kauracewa zuba jari a kasashen Afirka. Wajen kamfanoni 500 ne dai suka yi rijista a karkashin kungiyar, wadda ya ce duk da cigaba da nahiyar ke samu a fannin kasuwanci, kawo yanzu 'yan kasuwar jamus na dari dari da zuba jari a nahiyar. A cewar Liebing, China kadai ce ta ke cin karenta babu babbaka a nahiyar Afirka ta zuba jari kai tsaye kuma tana samun ci gaba.
Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung labari ta rubuta dangane da janye manufarta da gwamnatin kasar Isra'ila ta yi na korar baki 'yan kasashen Afirka. Jaridar ta cigaba da cewar, gwamnatin fraiminista Benjamin Netanyahu ta kasa kammala shirinta na korar dubban baki 'yan Afirka da ke jibge cikin kasar.
Ana bayyana hakan dai a matsayin gazawa a bangaren gwamnatin Netanyahu. Shekaru da dama kenan gwamnatin kasar ke fuskantar matsin lamaba daga jam'iyyun adawar kasar na bukatar ingiza keyar baki 'yan gudun hijira wanda akasarinsu 'yan Sudan da Eritriya ne. A watan Disamba ne dai majalisar dokokin Isra'ilar ta zartar da kudurin korar baki 'yan gudun hijira da basu da takardun izinin zama cikin kasar ko kuma a su fuskanci zaman kurkuku. An bada tayin tikitin jirgin barin kasar kyauta da tsabar kudi kimanin franc 3400, ga duk wanda ya yarda ya bar kasar. Sai dai kawo yanzu babu kasar da ta amince da karbar 'yan gudun hijirar, duk da cewar Ruwanda da Uganda su ne Isra'ila ta yi wa tayin.
Za mu karkare shirin da rikicin Janmhuriyar Demokradiyyar Kwango da ya ki ci ya ki cinyewa na lokaci mai tsawo. A labarinta mai taken "miliyoyin mutane ne ke ci gaba da tsere wa kasar sakamakon mumunar yakin basasa, amma duniya na nuna halin ko oho" jaridar der Freitag ta yi tsokaci ne dangane da labarin wani matashi mai shekaru 22 da ke samun kulawar wasu likitoci, da basu gaya masa cewar rayuwarsa ta wasu 'yan watanni kalilan ce saboda, harsashin bindigar da aka harbe shi da ita a kirjinsa ta hannun dama ya yi masa mummunar illa daga cikin jikinsa. A watan Disambar da ya gabata ne dai Kapitu ya samu mummunan rauni a lokacin da fada ya barke tsakanin mayakan wasu kabilu da ba sa ga maciji da juna. Ba kasafai ake samun labarin rikicin da kan auku a yankunan da ke cikin koguna masu nisa dake can yankin gabashin Kongon ba. Matashin na samun jinya ne a asibiti daya tilo dake kulawa da wajen mutane dubu 500 dake yankin Masisi, kuma yana cikin mawuyacin hali. Halin da kasar Kongon ke ciki dai batu ne da ke bukatar martanin gaggawa daga kasashen duniya, ganin cewar tamkar an manta da rikicin.