1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kamaru: Mataimakin shugaban kasa ko rikici?

Zakari Sadou SB
April 7, 2026

A Kamaru ana ci gaba da cece-kuce kan wanda shugaban kasa Paul Biya zai nada mataimakinsa yayin da Maurice Kamto ya kalubalanci kudirin dokar da ya ba shi damar nada wanda ya ga dama wanda hakan ya sabawa dimukuradiyya.

Shugaba Paul Biya na Kamaru
Shugaba Paul Biya na KamaruHoto: Etienne Mainimo/Matrix Images/IMAGO

Maurice Kamto shugaban jam'iyyar Mouvement pour la Rainassance du Cameroun (MRC) ya kaddamar da jadawali da ya bukaci yan Kamaru su bayyana ra'ayoyinsu dangane da kwaskwarima da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasa, wanda ya baiwa shugaban kasa damar nada mataimakin shugaban kasa wanda cikin sa'o'i daya yan kasar sama da dubu 8 suka kalubalanci kwaskwarimar da aka yi wa kudin tsarin mulkin kasar.

Gyara doka

Majalisar KamaruHoto: Etienne Mainimo/Matrix Images/IMAGO

Ranar 2 ga watan Aprilu yan majalisar dokoki da hadin gwiwar na dattawa suka amince da kudirin dokar da ya baiwa Paul Biya mai shekaru 93 a duniya wanda ya kwashe shekaru 43 yana mulkin kasar zaban wanda zai gaje shi.

Wannan kudirin dokar ya sabawa dimukradiya inji Maurice Kamto da aka yi fatali da takardunsa na tsayawa takarar zaben 2025.

Maurice Kamto dan adawa a KamaruHoto: AFP

Duk wannan na zuwa ne yayin da guguwar siyasar kasar ke kadawa kuma yan Kamaru na zaman jiran wanda Paul Biya zai nada a matsayin mataimakinsa sai dai gabatar da sunan dansa Emmanuel Franck Olivier Biya da magoya bayansa suka yi ya jawo cece-kuce tsakanin 'yan kasar saboda ba karo na farko bane da yan kungiyarsa Les Frankis suka fara bayyana shi a matsayin wanda ya dace ya gaji shugaban kasa ko da kuwa ra'ayin kasar ya banbanta mataimakin shugabar karamar hukumar Douala na 2 Zakari Yaou Ousseini ya ce ba laife bane idan Paul Biya ya zabi dansa a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Ba karon farko bane da shugaba Biya ke yi wa kudin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin ci gaba da dauwama kan madafunikon kasar sai dai wannan karon ya yi hakan ne domin samun mafita amma da jam'iyyarsa za ta ci gaba da tafiyar da siyasar kasar inji masu nazari akan harkokin siyasar kasar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani