Shari'a ce za ta yi halinta kan sakin Nnamdi Kanu
January 6, 2022A wani abun da ke shirin ta'azzarar muhawara ta siyasa da kila ma tsaron kasa, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya dauki lokaci yana amai bisa batutuwa da dama da suka shafi makoma ta kasar. Kama daga batun tsaro ya zuwa ga siyasar 2023 da uwa uba gwagwarmayar ballewa dai, Shugaba Buhari bai bar komai ba wajen ayyana ra'ayinsa bisa abin da ya shafi sassa daban-daban cikin kasar.
To sai dai kuma na kan gaba na zaman makomar jagoran neman ballewar Biafra, Nmandi Kanu da gwamnatin kasar ta sake kamawa a watan Yunin bara. Wasu dattawan kabilar ta Igbo ne dai tun da farkon fari suka nemi shugaban kasar ya sako Kanu bisa sharadin kai karshen gwagwarmayar da ta dauki lokaci kuma ke neman zama barazana mai girma ga makomar kasar.
Kafin sabuwar sanarwa ta shugaban da ke shirin sace gwiwa ta magoya bayan Kanun. Barrister Nnmeaka Ejeafor dai na zaman daya a cikin lauyoyin Kanu da kuma ya zargi kungiyar Miyyetti Allah da kasa kai wa ga tabbatar da 'yancin Kanu.
Can a baya dai shugabanni a kasar kama daga Olusegun Obasanjo ya zuwa ga Goodluck Ebele Jonathan sun saka baki wajen yafewa 'yan laifi na siyasar.