1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus a kan Afirka

Abdullahi Tanko Bala
October 5, 2024

Kwalliya ba ta biyan kudin sabulu dangane da kokarin dakile 'yan ci rani da ke kawarara zuwa Turai daga Afirka

Wasu 'yan gudun hijirar Afirka a iyakar Libya da Tunisia
Wasu 'yan gudun hijirar Afirka a iyakar Libya da TunisiaHoto: MAHMUD TURKIA/AFP/Getty Images

Ba'a amfani da biliyoyin kudaden da Turai ta ke kashewa ta hanyoyin da suka dace

Jaridar Welt Online ta ce asusun EU a kan dakile kaura daga Afirka na da nufin yakar dalilan da ke haifar da kaura daga Afirka zuwa Turai. Yanzu Kotun bincike ta Turai ta sake yin suka.

A cikin wani rahoto da aka gabatar a Luxembourg, Kotun binciken ta soki cewa albarkatun asusun na Euro biliyan biyar an rarraba su ne amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Wannan shi ne tsawatarwa na biyu da masu binciken na EU ke yi.

Wasu 'yan gudun hijira daga Afirka a iyakar Libya da TunisiaHoto: Hazem Ahmed/REUTERS

Tuni dai suka caccaki asusun a shekarar 2018 kan rashin amfani da kudi ta hanyar da ta dace wajen yaki da matsalolin rashin zaman lafiya, hijira da kuma kaura daga nahiyar Afirka.

Naman giwa don magance yunwa

Jaridar die Tageszeitung ta bude sharhinta kan yawan giwaye da Allah ya yi wa Zimbabuwe albarkatunsu da yawa, kuma tana fama da karancin abinci. Yanzu za a kashe giwaye 200.

Har zuwa kusan shekaru goma da suka gabata, ana daukar giwaye a matsayin nau'in dabbobi da ke cikin hadari. Sai dai a halin yanzu an samu karuwar yawan giwaye a Afirka. Amma Tinashe Farawo, da ke zama kakakin hukumar kula da namun daji ta Zimbabuwe ya ce suna shirin kashe giwayen wajen 200.

Giwaye a kasar NamibiaHoto: Wibke Woyke/Zoonar/picture alliance

Wannan mataki dai na da nasaba da matsanancin fari da aka shafe watanni ana fama da shi a kudancin Afirka. A halin da ake ciki, filayen ciyayi da ke cikin wuraren shakatawa na kasa, inda giwayen ke samun abinci, da kuma amfanin gonakin manoman da ke kusa da wuraren ajiyar yanayi sun bushe. Wannan yana haifar da rikici tsakanin dabbobin da mutane, saboda giwaye suna fita daga wuraren shakatawa suna cin amfanin gonakin manoma. Wasu giwayen sun zama masu tayar da hankali saboda yunwa.

Daga batun yunwa a yankin kudancin Afirka, sai kuma matsalar ambaliya a Yamma da Tsakiyar Afirka, inda sama da mutum 1000 suka mutu tun farkon wannan shekarar. Jaridar ta ci gaba da cewar, kasashen Najeriya da Mali da Chadi da kuma Nijar sun shafe makonni suna fama da ambaliyar ruwa, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Ambaliyar ruwa a Maiduguri NajeriyaHoto: Audu Marte/AFP

Ambaliyar ta yi awon gaba gidaje da muhimman gine gine. Fursunoni sun yi ta tserewa daga gidajen yarin da ambaliyar ruwa ta mamaye. Gawarwakin kada da macizai na ninkaya a tsakanin gawarwakin mutane a tituna. Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haifar da ambaliya mai girma a yankunan tsakiya da yammacin Afirka da ba a gani ba cikin shekaru masu yawa. Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke fama da rikici a Najeriya, na cikin wuraren da za su kasance cikin tarihi.

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,000 a yankunan tun daga farkon wannan shekarar tare da korar dubban daruruwan mutane daga gidajensu. Kasashen da suka fi fama da wannan bala'i daga indallahi sun riga sun shiga cikin matsalolin jin kai da suka hada da Najeriya da Mali da Chadi da kuma Nijar. A fadin Majalisar Dinkin Duniya dai a jimilce sama da mutane miliyan hudu ne ambaliyar ruwa ta shafa a yammacin Afirka ya zuwa yanzu.))