1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yuwuwar yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Hamas

Mahmud Yaya Azare SB/LMJ
November 21, 2023

Gwamnati Isra'ila tana tattaunawa game da yanayin da ake ciki na gaf da cimma yarjejeniyar 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su da kuma sakin fursinonin 'yan Hamas.

'Yan Isra'ila na nema ganin sakin wdaanda aka yi garkuwa da su
'Yan Isra'ila na nema ganin sakin wdaanda aka yi garkuwa da suHoto: Reuters

Kwanaki 45 bayan wani mummunan harin da kungiyar Hamas da wasu kasashen Yamma ke siffantata da ta 'yan ta'adda ta kai yankunan 'yan kama wuri zauna na Isra'ila ta halaka daruruwan mutane da yin garkuwa da wasu kimanin 260, mahukuntan Qatar sun sanar da cewa, ana gaf da cimma yarjejeniyar musayen fursnoniin da ake ci gaba da cece-kuce kanta.

Kabin Bayani: Gaza: Isra'ila ta mamaye asibitin Al-Shifa

'Yan Isra'ila na nema ganin sakin wdaanda aka yi garkuwa da suHoto: Reuters

Kamar yadda firaministan kasar Qatar, Sheikh Mohammed Bin Abdulrahman Al Thani ke fadi, duk da takaddamar da ake ta samu kan yarjejeniyar,cimma ta shi ne mafi maslaha ga bangarorin biyu. Da fari dai, kungiyar Hamas da Isra'ila da wasu kasashen Yamma ke siffantata da ta 'yan ta'adda, ta nemi da a yi ban gishiri in ba ka manda tsakanin dubban fursinoninta da ke garkame a gidajen yarin Isra'ila a madadin ta mika mutanen da ta yi garkuwa da su wadanda adadinsu yakai mutum 260, lamarin da Isra'ila ta yi fatali da shi.

To sai dai ci gaba da matsin lambar da Amurka ke yi wa Isra'ila kan ta yarda da yarjejeniyar musayen da za ta kai ga 'yanta 'yan kasarta kimanin bakwai da aka ritsa da su, da kuma salon tunzara 'yan Isra'ila da kungiyar ta Hamas ke dauka, ta hanyar nuna hotunan bidiyon wadanda take garkuwa da su, suna magiya ga mahukuntansu da su gaggauta amincewa da musayen da zai kai ga 'yanta su.

'Yan Gaza na tserewa zuwa kudancin yankinHoto: Rizek Abdeljawad/Xinhua News Agency/picture alliance

Wakazalika, ci gaba da samun mace-macen da Hamas ke ikirarin an samu daga cikin wadanda take tsare da sun, sakamakon hare-haren kan mai uwa da wabi na daukar fansa da Isra'ila ke yi kan zirin na Gaza da a yanzu haka suka kai ga halaka kimanin mutane dubu 13, duk wadannan sun sanya majalisar tsaron Isra'ila ta sanar da amincewarta da musayen fursinonin da kasar ta Qatar ke shiga tsakani don ganin an cimmar, duk kuwa da gunagunin da firaministan kasar Benjamin Netanjahu da wasu ministocinsa masu tsattsauran ra'ayi.

A daya bangaren, kungiyar Hamas, ta bakin kakakinta na harkokin waje, Isma'il Haniyya, ta ce ta amincewa da sharudanta na tsagaita buda wuta kafin fara musayen fursinoni daki-daki, gami da bude iyakokin zirin ba shinge ne kadai zai iya kai wa ga amincewarta da yarjejeniyar musayen.