Shin yarjejeniyar gabashin Kwango za ta yi aiki?
February 17, 2026
Yanzu haka masana na ci gaba da nuna shakku martaba yarjejeniyar, amma masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun na ganin Amurka na iya ciyar da shirin zaman lafiya gaba saboda kare muradunta a Kwango.
Yanayin da ke ƙara tabarbarewa a gabashin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango ya kasance babban abin damuwa ga 'yan siyasa da jami'an diflomasiyya a 'yan kwanakin nan.
Matsayin kasar Kwango
Shugaban Kwango Félix Tshisekedi ya aika da ministar harkokin Wajensa Thérèse Kayikwamba Wagner zuwa birnin Munich na Jamus a lokacin taron tsaro na duniya, domin tabbatar wa da hukumomin na Jamus cewa gwamnatin tana da niyyar martaba yarjejeniyar tsagaita wutar da aka sanar za ta fara aiki a ranar 18 ga watan Fabrairu.
Tun farko dai Shugaban Amurka Donald Trump ya shiga tsakani aka cimma yarjejeniyar tsagaita wutar a ranar 4 ga Disamba, na shekara ta 2025, a birin Washington tsakanin Kwango da Ruwanda.
Kwango da Amurka da MDD sun daɗe suna zargin Ruwanda, da tallafa wa ƙungiyar mayaƙan ‚yan tawayr ta M23, abin da Ruwanda ta sha musantawa akai-akai.
Matsayin gwamnatin Ruwanda
Yaƙin da ake yi a gabashin Kwango ya ci gaba da tsananta sama da shekaru 30. Ƙoƙarin zaman lafiya da aka yi a baya wanda Angola, da Kenya, daTogo, da Katar suka shiga tsakani bai haifar da wani sakamako mai ɗorewa ba Sai dai wannan jikon Ruwanda ta sha alwashin cimma shirin zaman lafiyar.
Shugaba Paul Kagame na Ruwanda bai hallara ba a Munich amma ministan cikin gidansa Vincent Biruta ya bayyana matsayin Ruwanda a kan rikicin na cewa Ba za su taba amincewa kan rashin martaba wannan yarjejeniya ba,daga dukanin bangarorin da suka yi alkawari a gaban shugaban Amurka.
Bangaren masana
Masana dai a kan sha‘anin tsaro na hasashen cewar da ker shirin tsagaita wutar ya samu karbuwa kamar yadda Timo Roujean, shugaban ofishin gidauniyar Konrad Adenauer da ke Kinshasa ya nunar da cewa gwamnati da mayakan M23 suna da wani nau'in kishin kasa.
Kamfanonin Amurka sun shirya manyan ayyukan albarkatun kasa a Manono a yankin Tanganyika. Kamfanonin suna da niyyar haƙar lithium da sauran ma'adinai a kann haka Amurka za ta yi duk abin da ta yi na takawa 'yan tawayen na M23 birki don hana su ci gaba da kame garuruwa.
Bayan kama garin Goma a cikin watan Janairu na shekara ta 2025, 'yan tawayen sun ci gaba zuwa Uvira. Amma saboda matsin lambar diflomasiyyar Amurka a kan Rwanda, M23 ta janye makonni biyu da suka gabata.
Ko da yake da wuya a ce bindigogin za su yi shiru a ranar 18 ga Fabrairu ba, diflomasiyya tana da damar warware rikicin. Bukatun tattalin arziki na Amurka da gwamnatin Kongo na iya inganta waɗannan damar.