1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labaran Afirka da ke jaridun Jamus

Usman Shehu Usman
January 27, 2023

Rikicin 'yan tawayen M23 a Kwango da ziyarar ministan harkokin wajen Rasha a Afirka ta Kudu da tallafin da Ukraine ta samu daga Afirka, sun dauki hankalin jaridun na Jamus.

Ministocin harkokin wajen Rasha da Afirka ta KuduHoto: Russian Foreign Ministry Press Service via AP

Sharhunan na wannan makon ya fara ne da jaridar die Tageszeitung, wadda ta ce kullum jiragen yaki na bude wuta. Jirgi mallakar Ruwanda ya yi luguden wuta a kan wani jirgin saman sojan Kwango, wannan shi ne jawaban da suka fito daga Kigali da Kinshasa. 

A daya bagaren kuma yakin da ake gwabzawa tsakanin sojojin Kwango da 'yan tawaye na kara kamari a ranar 26 ga watan Janairun 2023, a cewar jaridar. Shirin samar da zaman lafiya kafin rugujewar yarjejeniyar 'yan tawayen M23 na adawa da sojojin haya na Romaniya: Fada ya sake barkewa a tsaunukan da ke gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango. Yayin da gwamnatocin Kwango da Ruwanda kuwa suke zargin juna da wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta.

Sai kuma jaridar Süddeutsche Zeitung, wace ta ce tare da isar da manyan tankunan yaki daga Maroko, wata kasa ta Afirka ta tallafa wa Ukraine da makamai a karon farko. Sai dai fa wadannan tsoffin tankokin yaki ne na tun shekarun 1985 da aka kera lokacin tarayyar Soviet, kuma har yanzu ana kerawa a kasar Rasha.


Bari mu dora batun kasar Rasha, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce kyakkyawar ziyara. Tana mai cewa ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu Naledi Pandor ta yi wa  Sergei Lavrov takwaranta na Rasha kyakkyawar sani, kuma ta yi masa tarba mafi daraja lokacn da ya kawo ziyara.

Ministan harkokin wajen Rasha ya isa birnin Pretoria a wannan Litinin a wata ziyarar yini guda. A yayin ziyarar, Pandor ta yi magana game da "muhawarori masu amfani", shi kuwa Lavrov a martanininsa ya jaddada "tattaunawar siyasa ta yau da kullun tare da Afirka ta Kudu da fadada hadin gwiwa a cikin fannonin tattalin arziki, fasaha mai zurfi da bangaren aikin soja. Amurka da Birtaniya da kasashen EU sun toshe duk irin wannan tattaunawar.